Kim Jong Un Ya Harba Makami bayan Jin Motsin Amurka Kusa da Koriya ta Arewa

Kim Jong Un Ya Harba Makami bayan Jin Motsin Amurka Kusa da Koriya ta Arewa

  • Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami tekun Japan, kwanaki bayan ta yi gargadi kan atisayen sojan hadin gwiwa tsakanin Amurka a kusa da ita
  • Harin ya zo ne yayin da ake rade-radin yiwuwar haduwar shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa a China, lamarin da zai iya sake bude kofar tattaunawa
  • Sai dai gwamnatin Kim Jong Un ta soki kokarin zaman lafiya na baya-bayan nan, tana mai cewa ba za ta canza matsaya kan mallakar makaman nukiliya ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Koriya ta Arewa - Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami guda 10 zuwa Tekun Japan a ranar Asabar, 14 ga Maris 2026.

Rundunar sojin Koriya ta Kudu ta sanar da harba makaman kwanaki kadan bayan Pyongyang ta yi gargadin cewa za a fuskanci “mummunan sakamako” saboda atisayen sojan hadin gwiwa tsakanin Koriya ta Kudu da Amurka.

Kara karanta wannan

Yadda yakin Iran da Isra'ila zai amfani Najeriya da tattalin arzikinta

Kim Jong Un yayin gwajin makamai
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un a bakin teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta rahoto cewa a baya-bayan nan Pyongyang ta kawo cikas ga shirin kokarin samun sassaucin dangantaka ta diflomasiyya da Koriya ta Kudu da ke kawance da Amurka.

Adadin makaman da Koriya ta Arewa ta harba

Rundunar sojin Koriya ta Kudu ta ce ta gano kimanin makamai masu linzami guda 10 da ba a tantance ba da aka harba daga yankin Koriya ta Arewa zuwa Tekun Japan.

Ita NBC ta rahoto cewa ma’aikatar tsaron Japan ma ta tabbatar da harba makaman, inda ta wallafa cewa:

“Abin da ake zaton makami mai linzami ne aka harba shi daga Koriya ta Arewa.”

Sanarwar ta zo ne sa’o’i kadan bayan Firaministan Koriya ta Kudu Kim Min-seok ya ce Shugaban Amurka Donald Trump na ganin cewa haduwa da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un zai kasance “abu mai kyau.”

Shekaru da dama Amurka tana jagorantar kokarin dakile shirin makaman nukiliya na Koriya ta Arewa, sai dai tarurruka, takunkumi da matsin lamba na diflomasiyya ba su kawo wani gagarumin sauyi ba.

Kara karanta wannan

Rasha: Amurka ta fara bakin jini a Turai saboda yakin Iran

Batun ganawar Trump da Kim Jong Un

A watannin baya, gwamnatin Trump ta yi kokarin farfado da tattaunawa da Koriya ta Arewa, tana duba yiwuwar wani taro da Kim Jong Un a 2026, mai yiwuwa yayin ziyarar da Trump zai kai Beijing a watan Afrilu.

Firaministan Koriya ta Kudu da ya gana da Trump a Washington, ya ce Shugaban Amurka ya gaya masa cewa haduwa da Jong Un zai kasance abu mai kyau.

Shugaba Donald Trump a wajen taro
Shugaban Amurka, Donald Trump yana sauraron jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya fada a wata ziyarar da ya kai Asiya a watan Oktoban 2025 cewa yana shirye ya gana da Kim Jong Un, amma Koriya ta Arewa ba ta mayar da martani kan wannan batu ba.

Amurka ta kai hari a kasar Iran

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ya kai wani gagarumin hari Iran a daren Asabar.

A bayanin da ya yi, Donald Trump ya ce harin ya lalata wuraren da sojojin Iran ke zama a wani tsibirin da kasar ke hako danyen mai.

Shugaban Amurka ya yi gargadin cigaba da kai hare-hare Tehran, sai dai Iran ta ce za ta yi martani a kan duk harin da aka kai mata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng