Iran: An Harba Makamai Filin Jirgin da Amurka ke Aiki da Shi, Bakin Hayaki Ya Tashi
- Rahotanni sun nuna cewa wani mummunan hari ya afku a wajen da jiragen Amurka ke sauka da tashi a kusa da ofishinta da ke Bagadaza
- Hakan na zuwa ne bayan sanar da faduwar jirgin saman Amurka da mutuwar dukkan sojojin da ke cikinsa a wani bangare na kasar Iraq
- Dakarun Iran da masu goyon bayansu na cigaba da kai farmaki ofishin jakdancin Amurka a babban birnin Iraq tun bayan fara yakin da suka yi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iraq - Yayin da Amurka ke ikirarin cewa ta gama da Iran, an kai wani mummunan hari kan ofishin jakadancinta da ke babban birnin Iraq, Bagadaza.
Labarin ya zo ne jim kadan bayan Shugaba Donald Trump ya bukaci kasar Iran ta mika wuya, inda ya ce ya kai hari wajen da suke hako danyen mai.

Source: Getty Images
Rahoton da kamfanin dillancin labarai na AP ya fitar ya tabbatar da cewa wasu jami'an tsaron Iraq ne suka sanar da harin da aka kai wajen.
An kai wa Amurka hari a kasar Iraq
Rahotanni sun nuna cewa wani makami mai linzami ya afka kan filin saukar jirage masu saukar ungulu da ke cikin harabar ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza.
Hotuna da bidiyo aka fitar daga wajen sun nuna gagarumin hayaki yana tashi a sararin samaniya daga harabar ofishin jakadancin Amurka da safiyar Asabar.
Katafaren ofishin jakadancin ya kasance daya daga cikin manyan cibiyoyin jakadancin Amurka a duniya, ya sha fuskantar hare-haren rokoki da jiragen sama marasa matuki daga kungiyoyin mayaka masu goyon bayan Iran.
Kasar Amurka ba ta yi magana ba
Tashar 9 News ta wallafa cewa har yanzu ba a samu wani martani kai tsaye daga ofishin jakadancin Amurka da ke Bagadaza ba.
A ranar Juma’a, ofishin jakadancin ya sake sabunta gargadin tsaro a kasar Iraq kamar yadda ya saba bayan fara yaki a watan Fabrairun 2026.

Source: Getty Images
Ofishin ya yi gargadin cewa Iran da kungiyoyin mayaka masu goyon bayanta sun taba kai hare-hare kan ‘yan kasar Amurka, kadarorinsu da cibiyoyinsu, kuma za su iya ci gaba da kai irin wadannan hare-hare.
Amurka ta ce tana kai hare-hare
An kai harin ne a daidai lokacin da Ministan yakin Amurka, Pete Hegseth ya ce an kai hare-hare kan fiye da wurare 15,000 na abokan gaba, sama da 1,000 a kowace rana tun bayan fara yaki da Iran.
Ya kuma yi kokarin kwantar da hankulan jama’a kan batun toshe mashigar Hormuz, yana mai cewa:
“Mun riga mun dauki matakai kan wannan batu kuma babu bukatar a damu da shi.”
Iran ta kaiwa Amurka hai a Saudiyya
A wani labarin, kun ji cewa kasar Iran ta kai hari kan wani sansanin sojan Amurka da ke kasar Saudiyya, inda ta lalata jirage guda biyar.
Rahotanni sun nuna cewa jiragen da aka lalata a harin su ne masu dakon mai suna sakawa sauran jiragen saman Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.
An bayyana cewa wasu jami'an Amurka biyu ne suka tabbatar da kai harin, sai dai duk da haka sun kara da cewa ko mutum daya bai mutu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

