Iran Ta Yi Babbar Barna da Ta Harba Makamai kan Jiragen Amurka a Saudiyya

Iran Ta Yi Babbar Barna da Ta Harba Makamai kan Jiragen Amurka a Saudiyya

  • An samu karin hare-haren dakarun Iran kan sansanin sojan Amurka bayan, inda aka ce sun lalata jiragen yaki biyar a kasar Saudiyya
  • Runudnar sojin Amurka da ke kula da Gabas ta Tsakiya bata yi karin bayani ba game da harin da aka ce Iran ta kai kan jiragenta a yankin
  • Labarin kai harin ya fito ne bayan shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya kai hari kan wani tsibirin da Iran ke hako danyen mai cikin dare

Saudiyya - Rahotanni sun nuna cewa sansanonin sojan Amurka a Saudiyya na cigaba da fuskantar hare-hare daga dakarun kasar Iran.

Wani rahoto ya nuna cewa hare-haren makamai masu linzami sun latata wasu jiragen da Amurka ke amfani da su a Gabas ta Tsakiya.

Jirgin Amurka da Shugaba Donald Trump
Wani jirgin Amurka a hagu, Donald Trump a gefen dama. Hoto: US Central Command/Getty Images
Source: Facebook

Rahoton Wall Street Journal ya nuna cewa akalla jirage biyar Iran ta lalata a sabon harin da ta kai kasar Saudiyya a baya bayan nan.

Kara karanta wannan

Yaki da Iran: Wani babban jirgin dakon man Amurka ya rikito daga sararin samaniya

Iran ta lalata jiragen Amurka a Saudi

An lalata jiragen da ke dakon mai na rundunar sojin saman Amurka guda biyar yayin da suke sansanin soji na Prince Sultan da ke Saudiyya.

Rahotanni sun nuna cewa a ranar Juma’a, 13 ga watan Maris 2026 aka kai hari kan jiragen, kamar yadda aka nakalto daga wasu jami’an Amurka biyu.

Rahoton ya ce jiragen sun lalace ne sakamakon harin makamai masu linzami da Iran ta kai kan sansanin sojin da ke kasar Saudiyya a baya.

Duk da haka, ba a lalata jiragen gaba daya ba kuma ana kokarin gyara su sai aka sake kai musu hari a yanzu. Sai dai an ce babu wanda ya mutu a harin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce bai samu damar tabbatar da rahoton nan take ba, duk da cewa ya riga ya wallafa shi a shafinsa.

Sojojin Amurka 6 sun mutu

Hari kan jiragen Amurka a Saudiyya ya zo ne bayan rundunar sojin kasar ta ce jirgin soja mai dakon mai na KC-135 ya fadi a Yammacin Iraq.

Kara karanta wannan

Trump ya harzuka IRGC: Iran ta darkake jiragen dakon mai a cikin tekun Iraq

Jirgin ya fadi ne a ranar Alhamis, a wani lamari da rundunar sojin ta ce ya hada da wani jirgin sama na dabam, amma ba sakamakon harin makiya ko kuma kuskuren harbin abokan aiki ba ne.

Bayan faduwar jirgin, Amurka ta ce dukkan ma’aikatan jirgin sama guda shida da ke tafiya da shi sun mutu, inda ta ce za a saki hotunansu a gaba kadan.

Amurka ta tura adadi mai yawa na jiragen yaki zuwa Gabas ta Tsakiya domin su shiga ayyukan soja kan Iran baya yakin da aka fara.

Wani jirgin yakin Amurka
Yadda wani jirgin Amurka ke tafiya a sama. Hoto: US Central Command
Source: Facebook

Jirgin KC-135, wanda kamfanin Boeing ya kera a shekarun 1950 zuwa farkon shekarun 1960, ya dade yana zama ginshikin rundunar sojojin Amurka kafin fadowa a Iraq.

Trump ya kai babban hari Iran

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da kai wasu munanan hare-hare kasar Iran a ranar Juma'a da dare.

Ya bayyana cewa su kai harin ne a tsibirin Kharg da ke zama babban wajen da Iran ke hako danyen mai da jigilarsa zuwa kasashe.

Trump ya ce harin somin tabi ne matukar Iran ta cigaba da tsohe mashigar Hormuz, inda Tehran ta ce za ta dauki mataki kan duk harin da aka kai mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng