Nasara daga Allah: Kasar Musulunci Ta Iran Ta Kakkabo Jirage Fiye da 100

Nasara daga Allah: Kasar Musulunci Ta Iran Ta Kakkabo Jirage Fiye da 100

  • Sojojin kasar Iran sun yi ikirarin cewa sun kakkabo jirage marasa matuki 111 daga ranar da aka fara yaki da Amurka/Isra'ila zuwa yau
  • Rundunar sojin juyin juya halin Iran ta sanar da haka ne yayin da aka shiga rana ta 14 da fara musayar wuta a yakin Gabas ta Tsakiya
  • Daga daga cikin jiragen yakin Amurka da sojojin Iran suka kakkabo shi ne MQ-9 Reaper, wanda bayanai suka nuna yana da tsada

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Ana ci gaba da musayar wuta tare da yiwa juna barna yakin da ya barke tsakanin Amurka, wacce ta yi hadin gwiwa da Isra'ila da kuma kasar Iran.

A ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2028 aka fara wannan yaki bayan Amurka da Isra'ila sun fara kai wa Iran hari, wanda yau Juma'a, 13 ga watan Maris, 2026 ta zama rana ta 15.

Kara karanta wannan

Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a kasar Musulunci, fiye da mutane 1,400 sun rasu

Jirage.
Kananun jirage marasa matuka da ake amfani da su wajen yaki a Gabas ta Tsakiya Hoto: Anadolu
Source: Facebook

A wani rahoto da tashar Al-Jazeera ta tattaro, dakarun sojojin juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana wasu daga cikin nasarorin da suka samu a yakin zuwa yanzu.

Sojojin Iran sun sanar da cewa sun kakkabo jiragen yaki marasa matuki 111 tun bayan fara yakin da Isra'ila da kuma Amurka suka haddasa a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Iran ta harbo jirgin MQ-9 Reaper

Rahotanni sun nuna cewa rundunar kariyar sararin samaniyar Iran ta harbo wani jirgin yaki maras matuki na Amurka kirar MQ-9 Reaper a kusa da lardin Fars Province.

Haka kuma, sojojin sun yi ikirarin harbo wani jirgin sama kusa da birnin Tabriz, wanda hakan ya sa adadin jiragen da sojojin suka lalata ya kai 111, wadanda suka kunshi samfuri daban-daban.

Jirgin yaki samfurin MQ-9 Reaper na kasar Amurka na daga cikin jiragen leken asiri da kai hari mafi inganci a duniya.

Farashin jirgin Amurka da aka harbo

Kara karanta wannan

Rana ta 14: Iran ta jikkata dubban 'yan Isra'ila, an ji babban kara a Tehran

Bayanai sun nuka cewa farashinsa na kai Dala miliyan 30 zuwa 32, kwatankwacin kimanin Naira biliyan 42 zuwa 44 a kudin Najeriya.

Jirgin yana iya daukar makamai masu linzami kuma ana amfani da shi wajen leken asiri da kai hare-hare daga nesa.

Shugaban Iran.
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian tarw da wasu jami'an gwamnati Hoto: Jaafaru Hamid
Source: Getty Images

Saboda tsadarsa, wannan jirgi ya fi asalin jirage marasa matuki da ke iya kai hari sau daya,wadanda Iran ke amfani da su tsada sosai, cewar rahoton Vanguard.

Sai dai hukumomin Iran ba su bayyana cikakken bayani ba kan irin nau’ikan jiragen yakin da suka ce sun harbo, ko kuma nawa ne daga cikinsu na Amurka ko na Isra’ila.

China ta turo tallafin jin kai ga Iran

A baya, kun ji cewa kasar China ta bayyana cewa za ta bayar da tallafin $200,000 ga iyalan daliban da aka kashe a harin makami kan wata makaranta a Iran.

Gwamnatin China ya sake nuna damuwa da harin, wanda aka kai kan makarantar kananan yara tare da shi daruruwan dalibai a birnin Tehran.

Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce kasar a shirye take ta ci gaba da ba Iran duk wata taimako ta jin kai domin tallafawa al’ummar kasar a wannan lokaci mai wahala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262