Amurka Ta Saki Sunayen Shugabannin Iran da Take Farauta, Ta Sanya Ladar $10m
- Amurka ta sanya ladar dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanan sirri kan Mojtaba Khamenei da wasu manyan shugabannin sojojin Iran
- Daga cikin shugabannin da ake nema har da ministan leken asiri Esmail Khatib, Ali Asghar Hejazi, Janar Yahya Rahim Safavi, da sauransu
- Dakarun IRGC sun ce za su murkushe duk wani yunkuri na tada zaune tsaye a Iran yayin da Amurka ke cigaba da kakkabe manyan shugabannin kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Ma'aikatar Wajen Amurka, ta hanyar shirinta na "Rewards for Justice", ta yi kira ga jama'a da su bayar da bayanan sirri kan "shugabannin ta'addanci na Iran", ciki har da sabon jagoran ƙasar, Mojtaba Khamenei.
Amurka ta sanya ladan kuɗi har dala miliyan goma ($10m) ga duk wanda ya samar da sahihan bayanai, sannan ta yi alkawarin kwashe masu bayar da bayanan zuwa wata ƙasar daban domin tsira da rayukansu.

Kara karanta wannan
Amurka da Isra'ila sun yi babbar barna a kasar Musulunci, fiye da mutane 1,400 sun rasu

Source: Getty Images
Amurka na neman bayani kan shugabannin Iran
Sanarwar da aka wallafa a shafin 'Reward for Justice' na X, ta bayyana cewa waɗannan mutane da take nema, su ne suke ba da umarni ga sassa daban-daban na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC).
A cewar sanarwar, Amurka na zargin sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei da sauran shugabannin sojojin kasar su ne tsara ayyukan ta'addanci a faɗin duniya.
Ga jerin sunayen shugabannin Iran da Amurka take nema:
- Mojtaba Khamenei: Sabon babban jagoran ƙasar Iran.
- Esmail Khatib: Ministan Leken Asiri na Iran.
- Ali Asghar Hejazi: Mataimakin babban jami'in ma'aikata.
- Yahya Rahim Safavi: Manjo Janar a dakarun Iran.
- Eskandar Momeni: Birgediya Janar a rundunar sojin kasar Iran.
- Ali Larijani: Sakataren Majalisar Ƙoli ta Iran.
Haka kuma, Amurka tana neman bayanan mutanen da ke riƙe da waɗannan muƙamai: Sakataren majalisar koli kan tsaro, shugaban ofishin soji na jagoran addini, babban kwamandan dakarun IRGC, da kuma mai ba jagoran addinin Iran shawara.
Kalaman Trump kan sauyin gwamnati a Iran
A yayin wata tattaunawar manema labarai, Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa za a samu sauyin gwamnati a Iran, amma hakan ba zai faru cikin gaggawa ba, in ji rahoton Iran International.
Trump ya bayyana cewa babbar matsalar da ke hana mutane tunkude gwamnatin Iran ita ce yadda jami'an tsaro ke amfani da muggayen makamai wajen harbe fararen hula da ke zanga zanga.
Trump ya ce:
"Sun girke mutane a kan tituna dauke da manyan bindigogi, suna harbe duk wanda ya fito zanga zangar adawa da mulkin su."

Source: Getty Images
An hango Larijani a tattakin ranar Qudus
Duk da haka, ya nuna yaƙinin cewa matsin lambar da ake yi wa Iran daga waje da kuma taƙun saƙar da ake yi a halin yanzu zai kai ga rugujewar gwamnatin ƙasar a nan gaba.
A gefe guda, dakarun IRGC sun gargaɗi masu adawa da gwamnati cewa za su fuskanci martani mafi tsanani fiye da na baya idan suka sake fitowa zanga-zanga.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta ji ruwan wuta, ta fara karaya a shirin da ta yiwa gwamnatin Musulunci ta Iran
Duk da wannan barazana da kuma ladan kudin da Amurka ta sanya a kansa, Ali Larijani ya fito fili ya shiga tattakin ranar Al-Quds a birnin Tehran
Rahoto ya nuna cewa, Ali Larijani ya wallafa hotunansa a kafafen sada zumunta, don tabbatar da cewa 'ko gezau' neman da Amurka take masa.
An kashe kwamandojin Iran a Beirut
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojojin ruwan Isra'ila sun kashe manyan kwamandojin Iran guda biyar a wani hari da suka kai otal dake Beirut.
Kasar Isra'ila ta yi ikirarin cewa kwamandojin da aka kashe sun boye a cikin otal na fararen hula domin gudanar da ayyukan ta'addanci.
Sama da mutane 150, ciki har da jami'an diflomasiyya na Iran sun fice daga Lebanon sakamakon barazanar Isra'ila na ci gaba da kashe su.
Asali: Legit.ng
