Iran Ta Shiga Matsala: Bataliyar Sojojin Amurka Mai Hatsari Ta Bar Japan zuwa Gabas
- Amurka ta shirya tura bataliyar sojojin ruwanta masu hatsari zuwa Gabas ta Tsakiya domin kare jiragen ruwa a mashigar Hormuz
- Dakarun za su tashi daga kasar Japan a cikin jiragen yaki karkashin USS Tripoli domin karfafa ayyukan sojin Amurka kan kasar Iran
- Wannan runduna ta musamman tana da jiragen yaki da na kwashe mutane wadanda za su iya kai hare-hare ta cikin ruwa baki daya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Gwamnatin Amurka ta sanar da shirin tura wata runduna ta musamman ta mayakan ruwa zuwa yankin Gabas ta Tsakiya a daidai lokacin da yakin da ake fafatawa da Iran ke kara kazanta.
Rahotanni sun bayyana cewa Washington na shirin tura dakarun sojojin ruwan na MEU kusan 2,200 a cikin manyan jiragen ruwa guda uku domin karfafa ayyukan soji a yankin.

Kara karanta wannan
Yaki da Iran: Wani babban jirgin dakon man Amurka ya rikito daga sararin samaniya

Source: Getty Images
Amurka za ta tura sojoji 2,200 zuwa Gabas
Wani jami’in tsaron Amurka ya shaida wa kafar yada labarai ta Al Jazeera cewa dakarun za su tashi ne daga sansanin sojin ruwa dake Okinawa a kasar Japan.
Wannan runduna, wadda ta hada da kwararrun ma’aikata kusan 2,500, tana da ikon gudanar da ayyukan kwashe mutane da kuma kai hare-hare ta cikin ruwa idan bukatar hakan ta taso.
An rahoto cewa wannan mataki zai taimaka wajen mayar da martani ga hare-haren da Iran ke kai wa jiragen dakon mai a mashigar ruwar Hormuz.
Har zuwa yanzu, Tehran ta dage kan alkawarinta na dakatar da zirga-zirgar jiragen man fetur a wannan mashiga mai muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.
Kasar Amurka za ta tura dakarun ARG
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya amince da bukatar da babbar rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta shigar na tura rundunar "Amphibious Ready Group" (ARG).
Wannan runduna za ta kasance karkashin babban jirgin yakin ruwa mai suna USS Tripoli, wanda tuni aka bayyana cewa yana kan hanyarsa ta barin kasar Japan zuwa Gabas ta Tsakiya.
Akwai yiwuwar tura karin wasu rundunonin na ARG idan yakin ya ci gaba da tsananta, kamar yadda jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito.
Abin sani game da dakarun MEU
Rundunar MEU da aka tura Gabas ta Tsakiya tana daya daga cikin rukunin dakarun Amurka mafi hadari saboda yadda suke da komai na bukata ba tare da jiran tallafi daga waje ba.

Source: Twitter
Tana kunshe da muhimman sassa hudu:
- Bangaren umarni: Wannan shi ne hedkwatar da ke tafiyar da dukkan harkokin soji, sufurin sama, da dabarun yaki.
- Bangaren yaƙin ƙasa: Wannan sashen shi ne kashin bayan rundunar, wanda ke kunshe da bataliyar sojoji, manyan bindigogin atilari, da motocin yaki na cikin ruwa.
- Bangaren yaƙin sama: Ya na kunshe da jirage masu saukar ungulu daban-daban, jiragen yaki masu gudu, da kuma tsarin kariya daga hare-haren sama.
- Bangaren kai dauki: Wannan sashen yana samar da abinci, magunguna, gyaran motoci, da sauran bukatun yau da kullum na dakarun MEU
Wannan shiri na Amurka na nuna cewa tana shirye-shiryen fuskantar duk wani kalubale da zai iya tasowa muddin Iran ba ta janye daga barazanar da take yi wa hanyoyin kasuwancin duniya ba.
Amurka ta yi magana kan Mojtaba Khamenei
A wani labari, mun ruwaito cewa, Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce sun ruguza dukkan masana'antun kera makaman Iran kuma shugabannin kasar sun koma buya.
Hegseth ya yi ikirarin cewa sabon jagoran Iran Mojtaba Khamenei ya samu munanan raunuka da suka saba kamanninsa, shi ya sa har yanzu ba a ganshi a fili ba.
Wannan na zuwa ne bayan Khamenei ya fitar da sakon gargadi gargadi ga Amurka da ta rufe sansanonin sojinta muddin tana son kauce wa karin hare-hare a yankin.
Asali: Legit.ng

