Za a Yi Ruwan Bama Bamai kan Iran, Amurka Ta Fadi Halin da Khamenei Yake ciki
- Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce sun ruguza dukkan masana'antun kera makaman Iran kuma shugabannin kasar sun koma buya
- Hegseth ya yi ikirarin cewa sabon jagoran Iran Mojtaba Khamenei ya samu munanan raunuka da suka saba kamanninsa, shi ya sa ba a ganshi ba
- Wannan na zuwa ne bayan Khamenei ya gargadi Amurka da ta rufe sansanonin sojinta muddin tana son kauce wa karin hare-hare a yankin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi kakkausan raddi ga shugabancin kasar Iran a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar.
Hegseth ya bayyana cewa dakarun Amurka sun yi nasarar ruguza dukkan masana'antu da wuraren da Iran ke amfani da su wajen kera makamai masu linzami.

Source: Getty Images
Amurka ta caccaki shugabannin Iran
Wannan na nufin cewa a halin yanzu, sojojin Amurka suna fafatawa ne da ragowar makamai da jirage marasa matuka da Iran take da su a ajiye, ba tare da damar sake kera wasu ba, in ji rahoton Yahoo News.
Hegseth ya bayyana sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, a matsayin wanda "ba shi da daukaka", inda ya kwatanta shi da "bera" wanda ke buya a karkashin kasa saboda tsoro.
Ya jaddada cewa Amurka ta riga ta farmaki daukacin layukan samar da makamai, cibiyoyin kirkire-kirkire na tsaro, da masana'antun soji na Iran.
A cewarsa, shugabannin Iran suna cikin halin fargaba da rashin tabbas, suna buya a cikin ramuka kamar yadda dabbobi ke yi idan hankalinsu ya tashi.
Amurka ta yi ikirarin raunata Mojtaba Khamenei
Ministan tsaron ya yi ikirarin cewa sabon shugaban na Iran, Mojtaba Khamenei, ya samu munanan raunuka wadanda suka sauya fasalin fuskarsa sakamakon hare-haren Amurka da Isra'ila, in ji rahoton Sky News.
Hegseth ya kafa hujja da cewa jawabin farko da Mojtaba ya fitar tun bayan nada shi, wanda aka karanta a gidan talabijin na kasar, sako ne na rubutu kawai ba tare da muryarsa ko bidiyonsa ba.

Kara karanta wannan
Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu
Ya tambayi dalilin da ya sa kasar da take da kyamarori da na'urorin daukar sauti ba za ta nuna shugabanta ba idan har yana cikin koshin lafiya.
Halin da Iran take ciki ya dagule ne bayan kisan mahaifin Mojtaba, tsohon jagora Ayotallah Ali Khamenei, a hare-haren da aka kai kwanakin baya.

Source: Getty Images
Gargadin Iran ga kasar Amurka
Hegseth ya ce gwamnatin Iran tana kan rugujewa, kuma ba su da ikon sadarwa ko tsara ayyukan soji yadda ya kamata. Ya lashi takobin cewa Amurka za ta ci gaba da yin ruwan bama bamai a Iran ba tare da sassauci ko jin kai ba har sai sun cimma nasara baki daya.
A bangaren Iran kuwa, sakon da aka karanta a madadin Mojtaba Khamenei ya gargadi Amurka da ta gaggauta rufe sansanoninta dake yankin Tekun Fasha.
Sakon ya yi barazanar cewa duk kasar da ta amince ta karbi bakuncin Amurka za ta fuskanci hare-hare. Haka kuma, Iran ta lashi takobin daukar fansa kan kowane dan kasar da aka kashe.
Ana zargin Rasha na taimakawa Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, ministan tsaron Biritaniya ya bayyana cewa Rasha na marawa Iran baya wajen amfani da jirage marasa matuka domin yakar Amurka.

Kara karanta wannan
Yau Amurka ta shirya kai hare hare mafi muni kan Iran, "mazauna Tehran su shirya"
John Healey ya yi ikirarin cewa Rasha na tura wa Iran dabarun yaki da ta koya a yakinta da Ukraine domin rura wutar rikicin Gabas ta Tsakiya.
Wannan na zuwa ne yayi da Biritaniya ta kakkabo wasu jiragen Iran dake kokarin kai hari sansanonin soji yayin da yakin yake cigaba da tsananta.
Asali: Legit.ng
