Ana Azumin Ramadan, Isra'ila Ta Kashe Wani Babban Malamin Addinin Musulunci

Ana Azumin Ramadan, Isra'ila Ta Kashe Wani Babban Malamin Addinin Musulunci

  • Isra'ila ta jikkata wani babban limami a masallacin Nabatieh al-Fawqa a hare-haren da take kai wa kan dakarun kungiyar Hezbollah a Lebanon
  • Rahotanni sun nuna cewa limamin, Sheikh Hassan Ghandour ya rasu sakamakon raunukan da ya ji a harin da Isra'ila ta kai gidansa
  • Wannan na zuwa ne yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Isra'ila da Hezbollah su dakatar da hare-haren da suke kai wa juna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lebanon - Rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani babban malamin addinin musulunci, Sheikh Hassan Ghandour sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai kasar Lebanon cikin watan Ramadan.

Sheikh Hassan Ghandour, wanda ke jagorantar masallaci a garin Nabatieh al-Fawqa, ya rasu ne sakamakon raunukan da ya samu bayan wani harin sama da Isra’ila ta kai a gidansa a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Da gaske Netanyahu ya bata yayin yakin Isra'ila da Iran? An samu bayanai

Lebanon.
Wani wuri da Isra'ila ta kai farmaki a Kudancin Lebanon Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Isra'ila ta yi ajalin Sheikh Hassan a Lebanon

Rahoton da tashar Al-Jazeera ta tattaro ya nuna cewa ya ce limamin, wanda ke kudancin Lebanon, ya rasu ne bayan wasu kwanaki yana jinya saboda raunukan da ya samu a harin.

A lokaci guda, rahotanni daga yankin sun ce sojojin Isra’ila sun kai wasu hare-haren sama guda biyu kan garuruwan Qantara da Qabrikha a Kudancin Lebanon, yayin da rikicin ke kara tsananta a yankin.

Sojojin Isra’ila sun kuma ce sun kashe wani dan kungiyar Hezbollah mai suna Murtaza Sarour, wanda suka bayyana a matsayin daya daga cikin masu harba jirage marasa matuka na kungiyar, in ji rahoton Arise News.

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi tsagaita wuta

A yayin da rikicin ya shiga rana ta 11, Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi kira ga bangarorin biyu su dakatar da yakin da suke yi.

Yayin wata ziyara da ya kai birnin Beirut, Guterres ya ce dole ne a tsagaita wuta domin bai wa Lebanon damar zama kasa mai cikakken iko ba tare da katsalandan daga kungiyoyi masu dauke da makamai ba.

Kara karanta wannan

Yaƙin Iran/Isra'ila: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan ƙayyade farashin fetur

Guterres ya kara da cewa:

“Lokacin kungiyoyi masu dauke da makamai ya wuce. Wannan lokaci ne da ya kamata a bar kasashe masu cikakken iko su tafiyar da harkokinsu."
Antonio Guterres.
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres Hoto: United Nations
Source: Getty Images

Kiran na Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne yayin da rikicin tsakanin Isra’ila da Hezbollah ke ci gaba da barazana ga tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.

Baya ga Hezbollah, Isra'ila na ci gaba da musayar wuta da kasar Iran, lamarin da ke kara jefa Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya cikin mawuyacin hali.

Da gaske Firaministan Isra'ila ya bata?

A wani rahoton, kun ji cewa wasu rahotanni da ake yadawa a shafukan sadarwa sun yi ikirarin cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bace.

Sai dai binciken da aka gudanar ya nuna cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne kuma labari ne da aka kirkira danufin yaudarar mutane.

Rahotanni da sababbin hotuna sun tabbatar da cewa Benjamin Netanyahu yana nan a Tel Aviv kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukan ofishinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262