China Ta Tausaya wa Iraniyawa, Za Ta Tura Makudan Kudi na Tallafi ga Iran
- Gwamnatin China ta tausaya wa halin da Iraniyawa ke ciki yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin kasar da Isra'ila
- China ta sanar da ba da tallafin dubban daloli ga iyalan daliban da aka kashe a harin makami kan wata makaranta a Iran
- Tehran ta zargi Amurka da Isra’ila da kai harin da ya kashe mutane akalla 165 ciki har da yara ƙanana da mata
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Beijing, China - Gwamnatin China ta sanar a ranar Juma’a 13 ga watan Maris, 2026 cewa za ta ba da tallafin kudi a Iran.
Kasar China ta bayyana cewa za ta bayar da tallafin $200,000 ga iyalan daliban da aka kashe a harin makami kan wata makaranta a Iran.

Source: Getty Images
Beijing ta bayyana harin a matsayin wanda aka kai ba tare da tantancewa ba, yana mai cewa ya faru ne a farkon rikicin da ya barke a Gabas ta Tsakiya, cewar Al Jazeera.
Iran ta zargi Amurka da kisan dalibai
Gwamnatin Iran ta zargi Amurka da Isra’ila da kai harin makamin da ya afkawa makarantar da ke kudancin kasar a ranar farko ta yakin kasar da Isra'ila.
Rahotannin kafafen yada labarai na Iran sun ce an gudanar da jana’izar akalla mutane 165 da suka mutu a harin, ciki har da yara kanana.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba ta wata hanya mai zaman kanta.
China ta sanar da tallafin kudi ga Iran
Ma’aikatar harkokin wajen China ta ce hukumar agajin ga gaggawa ta kasar za ta ba da tallafin agajin gaggawa na dala $200,000 ga takwararta a kasar Iran.
An bayyana cewa kudin za a yi amfani da su ne wajen taimakon iyaye da iyalan daliban da suka rasa rayukansu a harin.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Guo Jiakun, ya bayyana harin a matsayin babban take dokokin jin kai na kasa da kasa.

Kara karanta wannan
Iran ta fadi sharadin tsagaita wuta kan Amurka, Isra'ila bayan kuskuren farmakinta
Ya ce kai hare-hare kan makarantu da yara kanana ya sabawa ka’idojin jin kai da kuma dabi’ar bil’adama.
Ya kuma kara da cewa China a shirye take ta ci gaba da ba Iran duk wani taimako ta jin kai domin tallafawa al’ummar kasar a wannan lokaci da ke ciki.

Source: Getty Images
Bincike sojojin Amurka kan hari a makaranta
Rahotanni sun nuna cewa binciken sojojin Amurka ya gano cewa wani makami mai linzami na Tomahawk ne ya bugi makarantar bisa kuskuren kai hari.
Sai dai Isra’ila ta musanta cewa tana da hannu ko kuma masaniya kan harin da ya faru, cewar rahoton Punch.
A nasa bangaren, shugaban Amurka, Donald Trump, da farko ya yi zargin cewa watakila Iran ce ke da alhakin harin.
Daga baya ya ce zai amince da duk sakamakon binciken da hukumomi za su gabatar game da abin da ya faru.
Yakin Iran/Isra'ila: Khamenei ya ba Iraniyawa tallafi
An ji cewa sabon jagoran addinin Musulunci a Iran, Mojtaba Khamenei ya yi jawabin farko tun bayan nada shi mukami.
Nadin Mojtaba Khamenei na zuwa ne bayan kisan mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026.
Shugaban ya sanar da tallafin kudi ga mutanen da gidajensu ko dukiyarsu ta lalace a hare-haren da aka kai a Iran.
Asali: Legit.ng

