Yaki Ya Yi Zafi, Amurka Ta Sake Rasa Dakarun Sojoji a Fagen Daga

Yaki Ya Yi Zafi, Amurka Ta Sake Rasa Dakarun Sojoji a Fagen Daga

  • Wani jirgin saman Amurka mai loda man fetur ga jiragen yaki a sararin samaniya ya gamu da hadari a yammacin Iraki
  • Kungiyar Islamic Resistance da ke kasar Iraki ta yi dauki alhakin kakkabo jirgin daga sararin samaniya duk da dai mahukunta ba su bayyana hakan ba
  • Daga cikin sojojin da ke cikin jirgin, wasu sun mutu yayin da ake ci gaba da kokarin ceto sauran da ba a gani ba

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Rundunar sojojin Amurka ta tabbatar da mutuwar wasu daga cikin dakarunta bayan jirginsu ya fado.

Rundunar sojojin ta tabbatar da cewa mutane huɗu daga cikin ma'aikata shida da ke cikin wani jirgin dakon man Amurka da ya yi haɗari a yammacin Iraki sun mutu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutane biyun.

Kara karanta wannan

Yaki da Iran: Wani babban jirgin dakon man Amurka ya rikito daga sararin samaniya

Wasu sojojin Amurka sun mutu
Sojoji dauke da gawar wani jami'an tsaron Amurka da ya mutu Hoto: Vice President, JD Vance
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar US Central Command ta fitar a shafinta na X a ranar Juma'a, 13 ga watan Maris 2026.

Jirgin saman Amurka ya yi hadari

Wani jirgin Amurka mai loda man fetur a sararin samaniya ya yi haɗari a yammacin Iraki ranar Alhamis.

Mahukunta dai sun ce jirgin ya yi hadari ne ba sakamakon harbin maƙiyi ko na kuskure daga abokanan tafiya ba ne.

Waɗannan mutuwar ta nuna samun kari a kan sojojin Amurka bakwai da aka riga aka kashe a matsayin ɓangare na ayyukan yakin da Amurka ke yi da kasar Iran.

Sojoji nawa suka mutu?

"Da misalin ƙarfe 2:00 na rana (lokacin ET) a ranar 12 ga Maris, wani jirgin Amurka mai loda mai nau'in KC-135 ya faɗi a yammacin Iraki."
"An tabbatar da mutuwar mutane huɗu daga cikin ma'aikata shida da ke cikin jirgin yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin aikin ceto."

Kara karanta wannan

Babbar magana: Babban jirgin daukar jiragen yakin Amurka ya kama da wuta, an samu bayanai

"Ana kan binciken yanayin da ya janyo faruwar lamarin. Sai dai kuma, rasa jirgin ba ya da alaƙa da harbin maƙiyi ko harbin kuskure daga abokanan tafiya."
"An sakaya sunayen sojojin har sai bayan sa'o'i 24 da sanar da danginsu na kusa."

Amurka ta tura jirage masu yawa zuwa Gabas ta Tsakiya don shiga cikin ayyukan yaƙi da Iran, kuma wannan lamari ya nuna haɗarin da ke tattare ba wai kawai da ayyukan yaƙin ba, har ma da loda wa jirage man fetur a sararin samaniya.

An yi ikirarin kakkabo jirgin saman Amurka a Iraki
Wani jirgin yaki na Amurka Hoto: @CENTCOM
Source: Twitter

An yi ikirarin kakkabo jirgin Amurka

Ƙungiyar Islamic Resistance Group da ke Iraki, wadda ke cikin ƙungiyoyin da Iran ke marawa baya, ta yi iƙirarin ɗaukar alhakin kakkabo jirgin loda man fetur ɗin na sojojin Amurka.

Tashar Reuters ta ruwaito a ranar Talata cewa kusan sojojin Amurka 150 ne suka ji rauni a yaƙin da Amurka da Isra'ila suke yi da Iran.

Labarin haɗarin jirgin ya zo ne a ranar da sojojin ruwa na Amurka biyu suka ji rauni bayan jirgin ruwan daukar jiragen yaki na USS Gerald Ford ya fuskanci gobara a cikinsa wadda ba ta da alaƙa da fafatawar yaƙi.

Kara karanta wannan

Trump ya fadi lokacin da zai dauki Amurka ta jefa kasar Iran cikin tsananin duhu

An farmaki Yahudawa a Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani matukin mota ya afka wajen ibadar Yahudawa a jihar Michigan da ke kasar Amurka.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa mutumin ya kutsa da motarsa ne cikin wata babbar majami’ar Yahudawa a jihar Michigan.

Hukumar FBI ta kasar Amurka ta ce ana gudanar da cikakken bincike game lamarin da ake gani a matsayin hari na musamman da aka shirya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng