Za a yi Makoki a Israi'ila, Trump na Yaki da Iran, an kai Hari kan Yahudawa a Amurka
- Wani matukin mota ya afka wajen ibadar Yahudawa a jihar Michigan da ke Amurka, lamarin da ya jawo musayar wuta da jami'an tsaro
- Rahotanni sun bayyana cewa motar ta kama da wuta a wajen ibadar, inda aka bukaci karin jami'an tsaro a wajen domin kare majami'ar
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana, inda ya yi Allah wadai da harin da ya ce ya yi muni matuka kuma za a dauki mataki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Jami’ai tsaro sun ce wani mutum ya kutsa da motarsa cikin wata babbar majami’ar Yahudawa a jihar Michigan a yammacin ranar Alhamis a Amurka.
Shugaban gundumar Oakland, Mike Bouchard, ya shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin ya kutsa da motarsa da karfi ya karya kofofin majami’ar Yahudawan Isra'ila da ke West Bloomfield.

Kara karanta wannan
Yaki da Iran: Wani babban jirgin dakon man Amurka ya rikito daga sararin samaniya

Source: Getty Images
BBC ta rahoto cewa jami’an tsaron majami’ar sun bude masa wuta yayin da yake tunkarar wurin, sannan suka fuskance shi a cikin motar.
Ana bincike kan harin Yahudawa a Amurka
Hukumar FBI ta kasar Amurka ta ce ana gudanar da cikakken bincike game lamarin da ake gani a matsayin hari na musamman da aka shirya.
Ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ta bayyana sunan wanda ake zargin a matsayin Ayman Mohamad Ghazali, dan shekara 41 da haihuwa.
Majami'ar Yahudawa ta kama da wuta
Shugaban gundumar Oakland ya ce an kai ‘yan sanda 30 asibiti sakamakon shakar hayaki yayin da majami’ar ta kama da wuta sosai. Ya kara da cewa bincike zai gano abin da ya haddasa gobarar.
Wajen ibadar na daya daga cikin manyan majami’un Yahudawa a Amurka kuma tana da makarantar kananan yara inda aka kwashe yara da dama cikin gaggawa yayin faruwar lamarin.
Jami’ar FBI mai bincike ta musamman, Jennifer Runyan, ta ce lamarin ya tayar da hankali matuka kuma abin bakin ciki ne sosai.
Bayanin da 'yan sandan Amurka suka yi
‘Yan sanda ba su bayyana yadda wanda ake zargin ya mutu ba, inda aka ce yana da wahala a gano dalilin mutuwarsa saboda motar ta kama da wuta.
Sun ce:
“Ba za mu iya cewa mene ne ya kashe shi a wannan lokaci ba,”
“Amma jami’an tsaro sun yi musayar wuta da shi.”
Maganar Donald Trump kan harin
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana a wani taro a Fadar White House a ranar Alhamis yana cewa ya aika sakon jaje ga al’ummar Yahudawa na Michigan da kuma dukkan mutanen Detroit.
Trump ya ce:
“Abu ne mai matukar muni.”
An nemi Tinubu ya yi watsi da Amurka
A wani labarin, kun ji cewa lauya mai kare hakkin dan Adam a Najeriya, Femi Falana ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake nazari kan alaka da Amurka.
Falana ya ce babu yadda za a yi Amurka da samar da cikakken tsaro a Najeriya, inda ya buga misali da wasu abubuwan da ke faruwa a duniya.
Lauyan ya nemi gwamnatin Najeriya ta yi koyi da kasar Iran wajen inganta tsaro, musamman a bangaren karfin sojoji da 'yan sanda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
