An Yi wa Sojojin Faransa Ruwan Wuta ana tsaka da Yakin Iran da Amurka
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an kai wani mummunan hari kan sansanin sojojin Faransa a wani yanki na kasar Iraq suna bakin aiki
- Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya tabbatar da harin a sanarwar da ya fitar, inda ya ce abu ne da ba za a amince da shi ba
- Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an kashe wani sojan Faransa nan take a harin, sannan wasu jami'ai sun samu raunuka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iraq - Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa wani sojan Faransa ya mutu a wani hari da aka kai a yankin Kurdawa da ke Arewacin Iraq.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da kasar Iran a Gabas ta Tsakiya tun karshen watan Fabrairun 2026.

Source: Getty Images
Rahoton da Al-Jazeera ta wallafa ya nuna cewa wasu sojojin Faransa sun samu rauni, inda shugaba Macron ya fito ya yi karin bayani.
An kashe sojan Faransa a kasar Iraq
Emmanuel Macron ya ce babban jami’in soja Arnaud Frion ya mutu yayin da yake aiki a yankin Erbil, a wani hari da ya bayyana a matsayin “abin da ba za a amince da shi ba”.
A wani sako da ya wallafa a dandalin X a ranar Alhamis, Macron ya ce:
“Kasancewar su a Iraq yana cikin tsarin yaki da ta’addanci. Yakin da ake yi a Iran ba zai zama hujjar kai irin wadannan hare-hare ba.”
Shugaba Macron ya kara da cewa wasu sojoji da dama sun jikkata tare da Frion, amma bai bayar da cikakken bayani kan halin da suke ciki ba.
Ya kara da cewa:
“Faransa na tare da su da kuma iyalansu.”
Dalilin zuwan sojojin Faransa Iraq
Sojojin Faransa sun fara kasancewa a yankin tun shekarar 2015 a matsayin wani bangare na kawancen kasa da kasa da ke yaki da kungiyar ISIS.
Wakilin Al Jazeera a Bagadaza, Mahmoud Abdelwahed, ya ce kungiyar Islamic Resistance in Iraq ta dauki nauyin harin da wasu hare-hare.
Ya ce:
“Mun fahimci cewa suna kai hare-hare kan kadarorin Amurka, sansanonin soja, har ma da ofishin jakadancin Amurka a Erbil, ofishin jakadanci a Bagadaza, da kuma sansanin Victory da ke kusa da filin jirgin saman Bagadaza.”

Source: Getty Images
Kungiyar Ashab Ahl al-Kahf, wadda ke goyon bayan Iran a Iraki, ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a cewa kadarorin Faransa a Iraki da yankin gaba daya za su kasance cikin barazana,
Sojan Amurka ya yi batan dabo
A wani labarin, kun ji cewa wani tsohon sojan Amurka, Janar William Neil McCasland ya yi batan dabo tun ranar Juma'a, 27 ga Fabarairun 2026.
A dukufa neman William Neil McCasland tun bayan batar da ya yi, inda hukumomi suka ce an tambayi daruruwan mutane amma babu labarinsa.
An sanar da cewa Janar McCasland ya kasance daya daga cikin manyan sojojin da suka yi aiki a Amurka kuma ya rike muhimmin mukami.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

