Mojtaba: Sabon Jagoran Iran Ya Fadi Abin da Yake Son Kasashen Larabawa Su Yi Wa Amurka
- A karon farko an ji duriyar sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, tun bayan nadin da aka yi masa biyo bayan kashe mahaifinsa
- Mojtaba Khamenei ya bayyana cewa Iran na son yin kyakkyawar alaka da dangantaka tsakaninta da makwabtanta
- Sabon jagoran addinin na Iran ya bukaci kasashen Larabawa da ke a Gabas ta Tsakiya kan su gaggauta rufe sansanonin sojojin Amurka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi kiran da a gaggauta rufe dukkan sansanonin sojojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.
Mojtaba Khamenei ya yi gargaɗin cewa idan ba rufe sansanonin ba, za su zama wuraren da Iran za ta ci gaba da kai wa hari.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta rahoto cewa Mojtaba Khamenei ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa na farko ga jama'a tun bayan karɓar jagorancin Iran a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026.
Wane gargadi Mojtaba Khamenei ya yi?
Mojtaba Khamenei ya ce Iran za ta ci gaba da farmakar wuraren ayyukan sojojin Amurka a yankin yayin da take ci gaba da kiyaye dangantakar da ke tsakaninta kasashe maƙwabta.
“Dole ne a gaggauta rufe dukkan sansanonin Amurka da ke yankin; in ba haka ba za a kai musu hari."
- Mojtaba Khamenei
Iran ta bukaci rufe sansanonin sojojin Amurka
Khamenei ya ƙara da cewa hare-haren da Iran ke kai wa, tana kai su ne a kan sojojin Amurka, ba wai kan kasashen yankin ba, tashar Sky News ta kawo rahoton.
“Dole ne makwabtanmu su fayyace matsayinsu game da waɗanda suka kai wa ƙasarmu abin ƙauna hari kuma suka kashe al’ummarmu.”
“Ina ba su shawarar su rufe waɗannan sansanonin cikin gaggawa, domin a yanzu ya kamata su gane cewa iƙirarin Amurka na samar da tsaro da zaman lafiya ba komai ba ne illa karya.”
“Muna da iyakokin ƙasa ko na ruwa da ƙasashe maƙwabta 15, kuma a koyaushe muna son kyakkyawar dangantaka mai amfani da dukkaninsu.”
"To sai dai kuma, tsawon shekaru maƙiyi ya kafa sansanoni a hankali, na soja da na kuɗi, a wasu daga cikin waɗannan ƙasashe domin tabbatar da mamaye yankin."
"A lokacin hare-haren baya-bayan nan, an yi amfani da wasu daga cikin waɗannan sansanonin sojojin."
"Kamar yadda muka yi gargaɗi a fili, kuma ba tare da ɗaukar wani mataki kan ƙasashen ba, mun farmaki waɗancan sansanonin ne kawai."
- Mojtaba Khamenei

Source: Facebook
Hare-haren Iran sun raunata mutane a Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa ma'aikatar lafiya ta Isra'ila ta bayyana adadin mutanen da suka samu raunuka sakamakon hare-haren Iran.
Ma'aikatar lafiyar ta bayyyana cewa adadin mutanen da suka raunata ya kusa mutum 3,000 tun farkon fara yaki da Iran.
Adadin mutanen da suka raunata sakamakon hare-haren makamai masu linzami na Iran ya haɗa da fararen hula da kuma sojoji.
Asali: Legit.ng

