Tsohon Janar a Gidan Sojan Amurka Ya Bata yayin da Yaki da Iran ke Kara Zafi
- Wani babban sojan saman Amurka da ya yi ritaya ya yi batan dabo ana dab da fara yakin da Donald Trump da Isra'ila suka kaddamar a Iran
- Hukumomi na cigaba da neman sojan mai suna William Neil McCasland da ya bata tun safiyar ranar Juma'a, 27 ga watan Fabrairun 2026
- An bayyana cewa Neil McCasland na daya daga cikin sojoji da suka rike muhimman mukamai a Amurka, lamarin da yasa aka dukufa nemansa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Wani babban janar na rundunar sojin saman Amurka mai ritaya wanda ya taba jagorantar wani sansani da ake dangantawa da UFO ya bata kusan makonni biyu da suka wuce.
A halin yanzu jami’an tsaro suna rokon jama’a su taimaka wajen gano shi, kamar yadda hukumomin gundumar Bernalillo da ke jihar New Mexico suka bayyana.

Source: Getty Images
Yaushe sojan Amurkan ya bata?
CNN ta wallafa cewa Janar mai ritaya na rundunar sojin sama, William Neil McCasland mai shekaru 68, ya bar gidansa da ke Albuquerque da misalin karfe 11 na safe a ranar 27 ga Fabrairu 2026.
Tun daga lokacin bai sake tuntubar iyalansa ko abokansa ba, kamar yadda hukumomi suka bayyana a cikin wata sanarwa ga manema labarai, kuma ya bar wayarsa a gida.
Babbar damuwa ita ce an bayyana cewa akwai wata matsalar lafiya da ba a fayyace ba da ta kara gaggauta neman sa domin kada ta tsananta.
Yadda ake neman soja a kasar Amurka
Jami’ai sun gudanar da bincike a unguwanni, sun yi hira da mutane tare da hada kai wajen gudanar da ayyukan neman sa domin gano inda yake.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa hukumomin da ya ke karkashin yankinsu sun tabbatar da cewa an tuntubi fiye da magidanta 600 a yankin da ya ke zaune.

Source: Getty Images
A bayanan da aka fitar game da shi, an ce McCasland yana da tsawo kafa 5, yana da farin gashi (Furfura) da idanu masu launin shudi.
An kuma bayyana shi a matsayin mutum mai son hawa tsauni, gudu da kuma tuka keke a yankin Northeast Heights na Albuquerque da kuma gefen tsaunukan Sandia.
Rahoton Yahoo News ya nuna cewa sanarwar ta ce:
“Saboda irin matsayinsa da kuma alakar da ya kulla a baya, ofishin BCSO na hada kai sosai da hukumomi da dama, ciki har da ofishin FBI na Albuquerque da kuma sansanin sojin saman Kirtland".
A cewar rundunar sojin saman kasar, McCasland ya rike wasu daga cikin muhimman mukamai masu matukar sirri a aikin soja a Amurka.
Iran ta jikkata sojojin Amurka 150
A wani labarin, kun ji cewa wani bincike ya nuna cewa Iran ta jikkata sojojin Amurka sama da 150 a hare-haren da aka kasashe daban-daban a Gabas ta Tsakiya.
Tun farkon fara yaki da Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026 shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ba makawa za a rasa dakaru a fagen daga.
Sai dai a rahoton da gwamnatin Amurka ta wallafa ta sanar da cewa sojoji 140 ne suka jikkata, guda bakwai kuma suka riga mu gidan gaskiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


