An Gano Kasashe 4 da Trump ke Lallabawa Su Shawo kan Iran Ta Bayan Fage

An Gano Kasashe 4 da Trump ke Lallabawa Su Shawo kan Iran Ta Bayan Fage

  • Kasashen duniya da suka hada da Pakistan na gudanar da tattaunawa a boye da jami’an Iran, suna matsa mata ta tattauna da Amurka
  • Hakan na zuwa ne bayan shafe sama da kwana 10 ana gwabza yakin da Amurka ta hada kai da Isra'ila suka kaddamar a kasar Iran
  • Duk da samun bayanan bayan fage da ke nuna ana kokarin neman a tattauna da Iran, Shugaba Donald Trump na nuna cewa yana samun nasara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Jami’ai daga kasashe hudu na kokarin shawo kan Iran domin ta fara tattaunawa da Amurka a shirin kawo karshen yakin da ya barke a Gabas ta Tsakiya.

Wasu rahotanni sun nuna cewa kasashen Musulmi hudu ne Amurka ke amfani da su domin shawo kan shugabannin Iran su hawu teburin sulhu.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Gazawar Isra'ila ta fito, Netanyahu ya fara korafi kan rashin kudi

Sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei
Mojtaba Khamenei da aka nada a matsayin sabon jagoran Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Jerussalem Post ta wallafa cewa wasu daga cikin wadanda suke da masaniya game da lamarin ne suka sanar da ita kasashen da Amurka ke aiki da su.

Kasashen da ke son shawo kan Iran

Rahotanni sun nuna cewa kasashen Musulmi hudu, Pakistan, Oman, Masar da Turkiyya, ne ake amfani da su a shirin shawo kan Iran.

Rahoton ya ce:

"Manyan jami’ai daga Oman, Masar, Pakistan da Turkiyya na gudanar da tattaunawa a boye da manyan jami’an Iran domin kokarin fara tattaunawa da gwamnatin Donald Trump."

Bayanai sun nuna cewa ana so a samu damar tattaunawa ne da nufin cimma yarjejeniya ko ma tsagaita wuta a kan yakin da aka fara a ranar 28 ga Farairun 2026.

Kusan duka wadannan kasashe na Larabawa ne face Pakistan da ke Kudancin Asiya. Haka zalika Masar ce kurum kasar da aka dauko daga yankin Afrika.

Iran ta ki shiga tattaunawa da Amurka

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Iran ta bukaci kasashe su fatattaki jakadun Amurka da Isra'ila

Sai dai a cewar majiyar, har zuwa yanzu Iran ta ki amincewa ta shiga tattaunawa kan wata yarjejeniya da za ta kai ga zama a teburin sulhu.

An bayyana cewa Iran tana rike da matsayinta mai tsauri tare da gabatar da wasu sharuda da ta ce dole ne su kasance cikin duk wata yarjejeniya da za a iya kullawa tsakanin Tehran da Washington.

Kasar Iran ta gindaya sharudda 3

A ranar Laraba,11 ga Maris, 2026, rana ta 12 da fara yakin, Iran ta gindaya sharuda uku domin kawo karshen rikicin, yayin da Amurka da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren sama a cikin kasar.

“Yayin da nake tattaunawa da shugabannin Rasha da Pakistan, na sake jaddada kudurin Iran na tabbatar da zaman lafiya a yankin,”

Inji shugaban Iran, Masoud Pezeshkian a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Ya kara da cewa:

“Hanya daya tilo ta kawo karshen wannan yaki ita ce amincewa da hakkokin Iran, biyan diyya, da kuma samar da tabbacin da zai hana sake kai hare-hare a nan gaba.”

Kara karanta wannan

Shugaban Faransa ya fara kokarin shawo kan Ikasar ran domin tsayar da yaki

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump a wani waje a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Isra'ila ta fara korafi a yaki da Iran

A wani labarin, mun kawo muku cewa kasar Isra'ila ta fara korafi game da rashin kudi a kasa da mako biyu da shiga yaki da Iran.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa yakin ya zama musu dole duk da yana tattare da kalubalen kudi.

Netanyahu da Ministan kudin Isra'ila sun ce akwai bukatar a ware kasafin kudi na musamman domin kara shiri game da yakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng