Magana Ta Fito: Barnar da Bama Baman Iran Suka Yi Wa Sojojin Amurka bayan Kai Hari

Magana Ta Fito: Barnar da Bama Baman Iran Suka Yi Wa Sojojin Amurka bayan Kai Hari

  • Bayanai na ta fitowa kan harin da Iran ta kani kan wani sojojin Amurka da ke kasar Kuwait a farkon fara yakin da ake yi
  • Harin wanda aka kai ta hanyar amfani da jirgi mara matuki ya yi barna sosai fiye da yadda aka bayyana tun da farko
  • Majiyoyi sun bayyana cewa sojoji da dama sun gamu da munanan raunuka sakamakon harin, inda wasu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Amurka - Iran ta kai hari ta hanyar amfani da jirgi mara matuki kan sojojin Amurka a farkon fara yakin da ake yi.

Harin wanda ya kashe sojojin Amurka shida a sa’o’in farko na yaƙin da ake yi da Iran ya fi muni fiye da yadda aka bayyana a baya.

Iran ta kashe sojojin Amurka
Gawarwakin sojojin Amurka da Iran ta kashe a Kuwait Hoto: Vice President, JD Vance
Source: Facebook

Harin Iran ya yi barna ga sojojin Amurka

Kara karanta wannan

Yau Amurka ta shirya kai hare hare mafi muni kan Iran, "mazauna Tehran su shirya"

Majiyoyi sun shaidawa tashar CBS News cewa mutane da dama sun samu raunuka da suka haɗa da raunin ƙwaƙwalwa, raunukan shigar karfe, da ƙonewa.

Aƙalla mutum ɗaya ya buƙaci a yanke masa gaɓar jiki.

Majiyoyi sun bayyana yanayi mai ban tsoro da hargitsi bayan harin da aka kai wa wata cibiyar ayyukan yaƙi a tashar jiragen ruwa ta Shuaiba da ke wajen birnin Kuwait a ranar 1 ga Maris, 2026.

Hayaki ya cika ginin cikin sauri, wanda hakan ya sa ceton waɗanda ke ciki ya zama abu mai wahala.

An kwantar da sojojin Amurka a asibiti

Fiye da sojoji 30 ne suka rage a asibitoci a daren ranar Talata, 10 ga watan Maris 2026 sakamakon raunukan yaƙi daga harin na Kuwait.

Mutum ɗaya yana asibitin Brooke Army Medical Center da ke San Antonio, 12 a Walter Reed Medical Center da ke kusa da birnin Washington, D.C., sai kuma kusan 25 a Landstuhl Regional Medical Center da ke Jamus.

Daga cikin waɗannan, kusan mutum 20 sun isa ne a cikin jirgin jigilar sojoji na C-17 a asibitin Landstuhl a ranar Talata tare da raunukan da sojoji suka ayyana a matsayin "na gaggawa" kuma waɗanda ke buƙatar a dauko.

Kara karanta wannan

Sanata ya fara kumfar baki da Saudiyya, UAE suka ki taya Amurka yakar Iran

A cewar uku daga cikin majiyoyin daga cikinsu akwai masu munanan raunukan ƙwaƙwalwa, mantuwa da wasu raunukan da suka shafi kwaƙwalwa.

An tura fiye da ma’aikatan lafiya 100 zuwa Landstuhl don ba da taimako, in ji ɗaya daga cikin majiyoyin.

Pentagon ta yi gum da bakinta

Jami’an ma’aikatar tsaro (Pentagon) da farko ba su bayyana yawan mutanen da suka ji rauni a harin na Kuwait ba, amma sun bayyana a ranar 1 ga Maris cewa mutane biyar sun ji rauni sosai sannan wasu da dama sun sami raunuka marasa tsanani.

Sojoji biyu sun ɓace bayan harin, inda daga baya aka tsinci gawarwakinsu a ƙarƙashin baraguzan gini, in ji majiyoyin.

Pentagon tana da tsarin sanar da iyalan sojojin da suka raunata, kuma tana ƙoƙarin kare su daga jin labarin girman raunukan ta hanyar sanarwar manema labarai.

Sojoji sun ayyana "rauni mai tsanani" a matsayin wanda "ke buƙatar kulawar likita, kuma hukumar lafiya mai iko ta tabbatar da cewa mutuwa na iya faruwa amma ba lallai ba ne ta faru a cikin sa’o’i 72."

Kara karanta wannan

Yaki na kara zafi, Trump ya ja da baya, ya ki tura sojoji Iran

Iran ta kashe sojojin Amurka a kasar Kuwait
Gawarwakin sojojin Amurka da aka dawo da su daga kasar Kuwait Hoto: Vice President, JD Vance
Source: Facebook

An tabbatar da raunata sojojin Amurka

A ranar Talata, rana ta 11 na yaƙin, kakakin Pentagon, Sean Parnell ya ce kusan sojojin Amurka 140 ne suka ji rauni zuwa yanzu, ba tare da bayyana inda ko yaushe aka ji raunukan ba.

"Mafi yawancin waɗannan raunukan marasa tsanani ne, kuma sojoji 108 tuni sun koma bakin aiki. Sojoji takwas har yanzu suna cikin jerin waɗanda suka ji rauni sosai kuma suna samun kulawar likita mafi girma."

- Sean Parnell

Masu magana da yawun Pentagon ba su ba da amsa nan take ba ga tambayoyin da aka yi musu ranar Talata game da raunukan sojojin ko kuma inda aka ji raunukan.

Iran ta kai hari mafi muni kan Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta kaddamar da hari mafi muni kan Isra'ila tun farkon fara yakin da ake yi.

Rundunar IRGC ta bayyana cewa ta harba makamai masu linzami a rukuni na 37 na farmakin 'Operation True Promise 4' da ta kaddamar.

Kara karanta wannan

Iran ta ce ta kashe sojojin Amurka 500 a luguden wuta da ta masu

Hare-haren mafi muni an kai su ne kan tsakiyar Isra'ila da birnin Tel-Aviv da wasu sansanonin sojojin Isra'ila da ke Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng