Jiragen Ruwan Isra'ila Sun Gama da Matsala cikin Teku a Hannun Dakarun Iran
- Rundunar dakarun kare juyin juya hali ta Iran IRGC), ta bayyana cewa ta kai hari kan wasu jiragen ruwa na dakon kaya wuta
- ORGC ta bayyana daga cikin jiragen akwai mallakar Isra'ila wanda ya yi kokarin wuce ta mashigar Strait of Hormuz ta hanyar yin basaja
- Ta bayyana cewa jiragen ruwan sun sha wuta ne bayan da suka yi biris da gargadin da dakarun ta suka yi musu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce dakarunta na ruwa sun buɗe wa wasu jiragen ruwa guda biyu wuta.
Rundunar ta bayyana cewa ta tsayar da jiragen ruwan a mashigar ruwa ta Strait of Hormuz bayan sun yi fatali da gargaɗin da aka yi musu.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na IRNA ya yaɗa a ranar Laraba, 11 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan
Yaki da Iran ya jawo bakin jini ga Isra'ila, Spain ta dauki mataki kan kasar Yahudawa
IRGC ta farmaki jiragen ruwan Isra'ila
Rundunar IRGC ta ce jirgin ruwan, wanda ta bayyana a matsayin mallakar Isra'ila ne kuma yake ɗauke da tutar ƙasar Liberiya, da kuma wani jirgin daban, an farmake su ne bayan sun "yi taurin kan wucewa ta mashigar Hormuz ba tare da izini ba".
Sanarwar ta ce jiragen sun yi biris da gargaɗi da sanarwar gaggawa da dakarun ruwa na IRGC suka bayar kafin a buɗe musu wuta tare da tsayar da su.
Iran ta gargadi Amurka da Isra'ila
Hedkwatar rundunar sojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta yi gargaɗin cewa Iran za ta sauya salon yaƙinta daga "mayar da martani" biyo bayan hare-hare zuwa kaddamar da "hare-hare akai-akai" kan makiyanta.
Kakakin rundunar, Ebrahim Zolfaqari, ya kuma ce Amurka ba za ta iya sarrafa farashin danyen mai ba.
“Ba za mu bar ko lita ɗaya ta mai ta isa ga Amurka, [Isra'ila] da abokan huldar su ba. Duk wani jirgin ruwa ko tankar mai da ta nufi wajen su za ta zama halattaccen wurin kai hari gare mu."
“Ku shirya wa gangar mai ta kai dala $200 saboda farashin mai ya dogara ne da tsaron yankin, wanda kuka dagula.”
- Ebrahim Zolfagari
Ana fargaba kan mashigar Hormuz
Ana kara samun fargabar cewa yaƙin na iya dakatar da zirga-zirga ta mashigar Hormuz, wadda wata hanya ce mai matuƙar muhimmanci ga samar da mai da iskar gas a duniya.

Source: Twitter
Lamarin da ya tura farashin danyen mai na Brent sama da kashi 20 cikin ɗari tun bayan fara rikicin, sannan tuni ya janyo tashin farashin litar mai a faɗin duniya.
Sojojin Amurka sun bayyana a ranar Talata cewa sun lalata jiragen dasa bama-bamai na Iran guda 16 a kusa da mashigar Hormuz.
Shugaba Donald Trump ya ce har yanzu babu wasu rahotanni tabbatattu da ke nuna cewa Iran ta fara dasa bama-bamai a hanyar wucewar, yanayin da masana suka yi hasashen faruwarsa tun kafin fara yaƙin.
Spain ta janye jakadanta daga Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa kasar Spain ta dauki matakin janye jakadanta daga Isra'ila saboda yakin da take yi da Iran.
Wata majiya daga ma'aikatar harkokin waje ta ce ofishin jakadancin Spain da ke Tel Aviv zai ci gaba da aiki ne ƙarƙashin wakilin wucin-gadi.
Wannan matakin dai ya nuna yadda dangantakar diflomasiyya ta yi tsami tsakanin kasashen guda biyu.
Asali: Legit.ng

