Yaki da Iran Ya Jawo Bakin Jini ga Isra'ila, Spain Ta Dauki Mataki kan Kasar Yahudawa
- Dangantakar diflomasiyya ta yi tsami tsakanin kasar Spain da Isra'ila tun bayan da aka kaddamar da hare-hare kan Iran
- Firaministan Spain, Pedro Sanchez, wanda ya sha sukat Isra'ila kan kashe Falasdinawa a Gaza ya yi Allah wadai da yakin wanda ya ce ko kadan bai kamata ba
- A ranar Laraba, 11 ga watan Maris 2026, gwamnatin Spain ta sanar da janye jakadanta daga kasar Isra'ila wanda hakan ya nuna tabarbarewar alaka tsakanin kasashen biyu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Madrid, Spain - Kasar Spain da ke yankin nahiyar Turai ta janye jakadanta daga Isra'ila a hukumance.
Wannan matakin na Spain na nuna kara tsamin dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Source: Twitter
Tashar Aljazeera ta ce wannan matakin ya bayyana ne a cikin sanarwar da gwamnatin Spain ta fitar a ranar Laraba, 11 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Rasha ta yi nasara, ta fi kowa amfana da yakin Iran da Amurka, Isra'ila
Spain ta janye jakadanta daga Isra'ila
Sanarwar ta tabbatar da matakin da gwamnati ta amince da shi a ranar da ta gabata, shafin Middle East Eye ya kawo labarin a Facebook.
Wata majiya daga ma'aikatar harkokin waje ta ce ofishin jakadancin Spain da ke Tel Aviv zai ci gaba da aiki ne ƙarƙashin wakilin wucin-gadi.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Bisa shawarar Ministan harkokin waje, tarayyar Turai, kuma bayan tattaunawa da majalisar Ministoci a taron ranar 10 ga Maris, 2026, na ba da umarnin soke naɗin Ms Ana María Sálomon Pérez a matsayin Jakadiyar Spain a kasar Isra'ila."
Spain na adawa da yakin Isra'ila kan Iran
Firaministan ƙasar Spain, Pedro Sanchez, na ɗaya daga cikin tsirarun shugabanni a Turai da suka kalli harin haɗin gwiwa na Amurka da Isra'ila kan Iran a matsayin "rashin adalci, inda ya bayyana cewa matsayin Madrid shi ne "a'a ga yaƙi".
Gwamnatin Sanchez ta kasance ɗaya daga cikin ƙalilan a ƙasashen Turai da suka dage wajen yin Allah-wadai da ayyukan Isra'ila a Gaza.

Kara karanta wannan
Bayan kwana 10 ana musayar wuta, Firaministan Isra'ila ya mika bukata 1 ga mutanen Iran
A watan Oktoban 2025, majalisar dokokin Spain ta amince da mayar da dokar takunkumin hana sayar wa Isra'ila makamai gaba ɗaya ta zama tabbatacciya.
Dokar ta haramta sayar da makamai, fasahar amfanin yau da kullum da ta soja, da kuma kayan yaƙi na dindindin a matsayin martani ga kisan kiyashin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa.

Source: Twitter
Spain ta taba janye jakadanta a Isra'ila
Gwamnatin Spain ta kira jakadanta tun a watan Satumban da ya gabata bayan da rikici ya tsananta tsakanin gwamnatocin biyu.
Taƙaddamar ta biyo bayan suka daga wajen Ministan harkokin wajen Isra'ila, Saar, kan wasu jerin matakai da Firaministan Spain, Sanchez, ya sanar.
Sanchez ya ƙaddamar da waɗannan matakan ne bayan ya yi Allah-wadai da kisan kiyashin da ake yi a Gaza.
Iran ta kai hari mafi muni kan Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar IRGC ta kasar Iran ta sanar da kaddamar da hari mafi muni kan kasar Isra'ila.
IRGC ta bayyana cewa ta harba makamai masu linzami zuwa tsakiyar Isra'ila da birnin Tel-Aviv da tsakiyar dare.
Hakazalika, rundunar ta bayyana cewa ta yi amfani da makamai masu linzami mabambanta a harin da ta kai.
Asali: Legit.ng