Iran/Isra’ila: Matakin da Ƴan Sanda Suka Ɗauka kan Shirya Zanga Zanga a London
- ’Yan sandan Birtaniya sun nuna damuwa kan shirin gagarumar zanga-zanga da ake shirin yi a birnin London da ke kasar
- Rundunar ta haramta zanga-zangar Al-Quds da ke goyon bayan Iran saboda gudun barkewar rikici a birnin London
- Jami'an 'yan sandan sun yi gargadin cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya haifar da tashin hankali da ba a yi tsammani ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
London, UK - ’Yan sandan Birtaniya sun sanar da haramta wata zanga-zanga da ake shirin yi a London.
An shirya zanga-zangar a ranar Lahadi 25 ga watan Maris, 2025 wadda ake dangantawa da masu goyon bayan Iran.

Source: UGC
Zanga-zangar Al-Quds ana shirya ta ne duk shekara a tsakiyar London karkashin kungiyar Islamic Human Rights Commission, cewar Reuters.
Musabbabin haramta zanga-zangar Iran a London

Kara karanta wannan
Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu
Hukumomi sun ce matakin hana zanga-zanga ba kasafai ake dauka ba a kasar Birtaniya, amma hadarin rikici tsakanin masu zanga-zanga da masu adawa ya yi tsanani sosai.
Sun kara da cewa haramcin ya shafi duk wani gangamin masu adawa, saboda fargabar barkewar rikici yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara dagula yanayi.
’Yan sanda sun ce a baya an kama wasu mutane a irin wadannan tarurruka saboda goyon bayan kungiyoyin ta’addanci da kuma aikata laifukan kyamar Yahudawa.
Sanarwar ta ce:
“Mun yi la’akari da yiwuwar tasirin da rikicin da ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya zai iya yi kan zanga-zanga, inda gwamnatin Iran ke kai hare-hare kan kawayen Birtaniya da kuma sansanonin sojoji a ƙasashen waje.”

Source: Twitter
Matsalolin da zanga-zangar za ta haifar
Hukumomin tsaro sun kuma nuna damuwa kan barazanar da gwamnatin Iran ke iya haifarwa a cikin Birtaniya, musamman yayin da take kai hare-hare kan kawancen Birtaniya.
Tun bayan harin Hamas kan Isra’ila a ranar 7 ga Oktobar shekarar 2023, an rika sukar yadda ‘yan sanda ke kula da manyan zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a London, cewar BBC.
A makon da ya gabata kuma, ‘yan sandan Birtaniya sun kama wasu maza hudu bisa zargin taimaka wa jami’an leken asirin Iran wajen sa ido kan mutane da wurare na Yahudawa a London.
Sai dai ‘yan sanda sun ce idan masu shirya zanga-zangar suka yi taron a wuri daya maimakon tafiya a titi, za a sanya masu tsauraran sharudda domin tabbatar gudanar da shi cikin kwanciyar hankali.
Isra'ila ta zargi Iran da yi mata kutse
Tun farko, kun ji cewa Isra’ila ta zargi Iran da kutsawa cikin kyamarorin tsaro da dama domin leƙen asiri tun bayan barkewar yakin Gabas ta Tsakiya.
Kamfanin tsaron yanar gizo na ya ce masu kutse sun yi amfani da kyamarori domin tattara bayanai kan wuraren da suke kai hari wanda ya jawo asara mai yawa.
Rahoto ya ce Isra’ila ma ta taba yin kutse a kyamarorin zirga-zirga a Tehran kafin harin da ya kashe Ali Khamenei a ranar Asabar 28 ga watan Fabrairun 2026.
Asali: Legit.ng
