Yadda Bama Baman Iran Suka Jikkata Sojojin Amurka 150 a Fagen Yaki

Yadda Bama Baman Iran Suka Jikkata Sojojin Amurka 150 a Fagen Yaki

  • Ana cigaba da samun bayanai game da illar da Iran ta yi wa Amurka/Isra'ila a yakin da aka shafe sama da kwana 10 ana yi a Gabas ta Tsakiya
  • Hare-haren da kasar Iran ta kai kasashen da Amurka ke da sansanonin soji ya kashe sojoji da raunata sama da 100 a cikin dakarun Washington
  • Tuni aka mayar da gawar wasu daga cikin sojojin Amurka zuwa gida daga Gabas ta Tsakiya, inda shugaba Donald Trump ya karbi wasu daga cikinsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Akalla sojojin Amurka 150 ne suka jikkata a cikin kwanaki 10 na yakin da ake yi da Iran, kamar yadda wasu mutane biyu da suka san lamarin suka shaida a ranar Talata.

Rahotanni sun nuna cewa dama Donald Trump ya shaida wa Amurkawa cewa ba a yaki ba tare da asarar rayuka ba yayin da ya ke kare matsayar da ya dauka ta shiga yaki da Iran.

Kara karanta wannan

Trump ya sake maganar kawo karshen yaki da Iran, ya yi wa duniya albishir

Yadda aka dauko gawar sojan Amurka
Gawar sojan Amurka da aka dauko daga Saudiyya zuwa gida. Hoto: Vice President JD Vance
Source: Facebook

Reuters ta rahoto cewa ma'aikatar yakin Amurka ce ta ce sojoji 140 suka samu raunuka yayin da wasu rahotanni suka ce wadanda suka jikkata sun kai 150.

Iran ta jikkata sojojin Amurka 150

Amurka ta bayyana illar da makaman da Iran ta harba sansanoninta a kasashen Gabas ta Tsakiya suka mata, inda aka ce sojoji 150 sun jikkata.

Ba a taba bayyana adadin wadanda suka jikkata ba sai da aka samu rahoton da ya ce sojojin Amurka 150 ne suka samu raunuka a yakin.

Kafin bayyana wannan adadi, ma’aikatar yakin Amurka ta Pentagon ta taba sanar da cewa sojoji takwas ne kawai suka samu munanan raunuka.

Bayan fitowar rahoton, Pentagon ta fitar da wata sanarwa inda ta kiyasta cewa kusan sojoji 140 ne suka jikkata, ta kuma ce mafi yawan raunukan ba su da tsanani.

Wasu sojoji sun koma bakin aiki

Babban kakakin Pentagon, Sean Parnell, ya ce tun bayan fara yaki da Iran, kusan sojojin Amurka 140 ne suka jikkata cikin kwanaki 10 na hare-hare da ake ci gaba da kaiwa.

Kara karanta wannan

An harba rokoki kan dakarun Isra'ila, sojojin Netanyahu sun mutu

Rahoton ABC News ya tabbatar da cewa Parnell ya ce daga cikin sojojin da suka jikkata, kimanin dakaru 108 sun riga sun koma bakin aikinsu.

Wasu sojojin Amurka da suka rasu
Wasu sojojin Amurka da Iran ta kashe a Kuwait. Hoto: @HouseGOP
Source: Twitter

Parnell ya kara da cewa sojoji takwas da suka samu munanan raunuka na samun kulawar likitoci a yanayi mafi dacewa.

Har yanzu ba a san irin raunukan da sojojin suka samu ba, ko kuma ko akwai wadanda suka samu matsalar kwakwalwa sakamakon fashewar bama-bamai.

Iran ta nemi korar jakadun Amurka

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin Iran ta kafa wa kasashen duniya sharadin wucewa da tankar mai ta mashigar Hormuz da ta toshe.

Rahotanni sun nuna cewa Iran ta nemi duk kasar da ta ke so ta wuce ta wajen dole ta kori jakadun Isra'ila da Amurka da yanke alaka da ita.

Hakan na zuwa ne bayan shugaba Donald Trump ya yi barazanar kai hare-hare masu zafi Iran idan ta cigaba da toshe hanyar jigilar mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng