Ana Wata ga Wata: Sojojin Iran Sun Ja Kunnen Trump kan Neman Tsayar da Yaki

Ana Wata ga Wata: Sojojin Iran Sun Ja Kunnen Trump kan Neman Tsayar da Yaki

  • Shugaba Donald Trump ya yi barazanar kara tsananta matakin soja a kan Iran idan Tehran ta yi yunkurin hana jigilar mai ta mashigin Hormuz
  • A lokaci guda kuma Trump ya bayyana cewa rikicin na iya zuwa karshe da wuri fiye da yadda aka zata cewa zai dauki makonni a karon farko
  • Sai dai dakarun juyin juya halin Iran (IRGC) sun yi martani ga Trump tare da bayyana cewa ba shi ke da ikon dakatar da yakin ba kwata-kwata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta yi saurin mayar da martani ga Donald Trump, inda ta yi gargadin cewa ba za ta bari ko litar mai daya ta fita daga yankin ba idan har hare-haren Amurka da Isra’ila suka ci gaba.

Kara karanta wannan

Amurka ta taɓo China a yaƙin Iran, ta tura gargaɗi kan rufe mashigar Hormuz

Hakan na zuwa ne bayan shugaba Donald Trump ya yi barazanar kai hari mai muni Iran idan aka cigaba da toshe mashigar Hormuz.

Masoud Pezeshkian da Shugaba Donald Trump
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian a hagu, Shugaba Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta wallafa cewa musayar kalamai masu zafi tsakanin Shugaban Amurka da Gwamnatin Iran ta kara tayar da hankalin duniya, lamarin da ya jawo sauye-sauye masu tsanani a farashin makamashi.

Martanin Sojojin Iran ga Donald Trump

Rundunar IRGC ta mayar da martani kan kalaman Trump game da lokacin da yaki zai kare, tana mai cewa Tehran ce za ta yanke hukuncin karshe ba Washington ba.

Kakakin rundunar Birgediya Janar Ali Mohammad Naeini ya bayyana kalaman Trump a matsayin “karya”, yana mai cewa shugaban Amurka na kokarin “kirkirar nasarori” bayan shan kunya a filin yaki.

A cewarsa:

“Mu ne za mu yanke hukuncin lokacin da wannan yaki zai kare,”

ND TV ta rahoto ya kara da cewa,

“Mun san cewa harsashinku ya kusa karewa kuma kuna neman hanyar fita daga yakin cikin mutunci. Me ya sa ba ku gaya wa jama’ar Amurka gaskiya ba?
"Trump ba ya son ‘yan Amurka su sani cewa dukkan kayayyakin sojin Amurka a yankin Tekun Fasha sun lalace.”

Kara karanta wannan

Iran ta fusata, ta kai hare hare Dubai, Saudiyya, mutane sun mutu

Iran ta ce tana da makamai har yanzu

Naeini ya kuma musanta ikirarin Trump cewa hare-haren Amurka da Isra’ila sun rage karfin makaman roka da kasar Iran ta mallaka.

Ya ce a yanzu ana harba karin makamai fiye da kwanakin farko na yakin, kuma adadinsu ya fi yawa a yanzu, ya ce suna da tarin makamai.

Wasu dakarun sojojin Iran
Dakarun IRGC na kasar Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Naeini ya kara da cewa rundunar sojin Iran ba za ta ba da damar fitar da ko lita daya na mai daga yankin zuwa kasashen da suka kai musu hari ba har sai an sanar da wani sabon mataki.

Gwamnatin Trump na cikin fargaba

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin shugaba Donald Trump na kokarin ganin yadda za ta magance matsalar tashin farashin mai a duniya.

Tashin farashin mai ya samo asali ne daga yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kasar Iran a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026.

Manyan jami'an gwamnatin Trump sun yi zama a karshen makon da ya wuce da kuma jiya Litinin domin lalumo hanyar magance matsalar.

Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng