Trump Ya Yi Maganar Tsayar da Yaki da Iran bayan Zaben Magajin Khamenei

Trump Ya Yi Maganar Tsayar da Yaki da Iran bayan Zaben Magajin Khamenei

  • Shugaba Donald Trump ya yi magana game da tsayar da yaki da Iran da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a ranar 28 ga Fabrairun 2026
  • Trump ya fadi rawar da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu zai taka kafin Amurka ta yi matsaya ta karshe game da dakatar da yakin
  • Shugaban Amurka ya yi maganar ne a wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho jim kadan bayan zaben magajin Ayatollah Ali Khamenei

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana kan yiwuwar tsayar da yaki da Iran a wata hira da ya yi a ranar Lahadi, 8 ga Maris 2026.

Tun ranar 28 ga Fabrairun 2026 Amurka da Isra'ila suka kaddamar da hare-hare Iran, lamarin da ya jawo mutuwar shugabannin kasar da dalibai mata..

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran

Donald Trump da Benjamin Netanyahu
Donald Trump na gaisawa da Benjamin Netanyahu a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A wata hira da Times of Israel ta yi da Donald Trump, shugaban Amurka ya yi bayani game da abin da Isra'ila za ta yi idan aka tsayar da yakin.

Iran: Maganar Trump kan tsayar da yaki

Shugaban Amurka Donald Trump ya shaida cewa shawarar lokacin da za a kawo karshen yaki da Iran za ta kasance ta hadin gwiwa, wacce zai yanke tare da Benjamin Netanyahu.

A cikin gajeruwar hira, Trump ya cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta lalata Isra’ila da shi da Netanyahu ba su kasance ba.

Rahoton Reuters ya nuna cewa Trump ya ce:

“Iran na shirin lalata Isra’ila da duk abin da ke kewaye da ita… Mun yi aiki tare. Mun lalata wata kasa da ta so ta rusa Isra’ila.”

Rawar Isra'ila a tsayar da yaki da Iran

An tambayi Shugaban Amurka ko shi kadai ne zai yanke shawarar lokacin da yakin da Iran zai kare ko kuma Netanyahu ma zai samu damar tofa albarkacin baki:

Kara karanta wannan

Yaki na kara zafi, Trump ya ja da baya, ya ki tura sojoji Iran

“Ina ganin shawara ce ta hadin gwiwa. Mun kasance muna tattaunawa. Zan yanke shawara a lokacin da ya dace, amma za a yi la’akari da komai,”

In ji shi, yana nuna cewa Netanyahu zai ba da gudummawa, amma shugaban Amurka ne zai yanke hukuncin karshe.

Firaministan Isra'ila a wajen da aka lalata
Benjamin Netanyahu a wani waje da aka kaiwa hari. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Isra'ila za ta cigaba da yakar Iran?

Da aka tambaye shi ko Isra’ila za ta iya ci gaba da yaki da Iran ko da bayan Amurka ta yanke shawarar dakatar da hare-harenta, Trump bai so ya yi tsokaci sosai kan haka ba, amma ya ce:

“Ba na tsammanin hakan zai zama dole.”

Kasar Rasha na taimakon Iran

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani rahoto ya ce kasar Rasha na taimakawa Iran da bayanai a yakin da ta ke da kasashen Amurka/Isra'ila.

Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa Rasha na ba Iran bayanai game da motsin jiragen Amurka da sojojinta a Gabas ta Tsakiya.

A daya bangaren, an bayyana cewa China na kokarin ganin lamura sun daidaita, inda aka ce ita ma za ta iya tallafawa Iran amma babu tabbas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng