Ramadan 2026: Saudiyya Ta Ayyana Ranakun Hutun Ƙaramar Sallah
- Hukumomin kasar Saudiyya sun fitar sanarwa game ranakun gudanar da sallar idi a wanann shekara ta 2026
- Ƙasar ta sanar da hutun idin karamar sallah ga ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu domin ba su damar shirya bukukuwa
- Ranar idi za ta dogara ne da ganin jinjirin watan Shawwal; idan Ramadan kwanaki 29 ne, Sallah za ta fara 19 Maris, 2026
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Riyadh, Saudiyya - Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hutun idi na shekarar 2026 ga ma’aikatan gwamnati.
Sanarwar na zuwa ne yayin da ake shirin kammala azumin watan Ramadan da ake yi a yanzu a fadin duniya.

Source: Facebook
Kwanaki nawa aka ba da hutu a Saudiyya?
Sanarwar ta fito daga Ma’aikatar Albarkatun Dan Adam da Ci gaban Jama’a wadda ta bayyana ranar fara hutu da tsawonsa bisa dokokin aiki da ake bi, cewar Saudi Gazette.
A cewar ma’aikatar, hutun ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyi masu zaman kansu zai fara bayan kammala aiki ranar Laraba 18 ga Maris.
Za su ci gaba da hutun na kwanaki hudu har zuwa ranar Asabar 21 ga Maris, kafin su koma aiki bisa jadawalin da kamfanoninsu suka tanada.
Game da ma’aikatan gwamnati, galibi ana fitar da jadawalin hutunsu ta takardun hukuma, kuma su ma kan samu kwanaki da dama domin bikin karshen watan Ramadan.
Sanarwar ta taimaka wajen daidaita shirye-shirye tsakanin bangarori daban-daban domin iyalai su tsara tafiya, ziyara da bukukuwan Sallah tun da wuri.
Idin karamar salla ita ce ranar farko ta watan Shawwal a kalandar Musulunci wadda ke zuwa bayan kammala azumin watan Ramadan.
Hasashen ranar da za a yi salla
Duk da haka, ainihin ranar Sallah na dogara ne da ganin jinjirin watan Shawwal wanda kwamitocin duban wata ke tabbatarwa a hukumance.
Idan Ramadan ya cika kwanaki 29, ana sa ran Sallah za ta fara ranar Alhamis 19 ga Maris shekarar 2026, cewar Times of India.
Amma idan ba a ga jinjirin ba, watan Ramadan zai cika kwanaki 30, sannan Sallah za ta fara ranar Juma’a 20 ga Maris.
Saboda kalandar Musulunci ta dogara da wata, ranakun bukukuwan addini kan canza a kalandar Miladiyya, shi ya sa sanarwa tun da wuri ke da muhimmanci.

Source: Getty Images
Shirye shiryen karamar Sallah
A halin yanzu, shaguna, filayen jiragen sama da kasuwanni a biranen Riyadh, Jeddah da Dammam na sa ran karuwar zirga-zirga yayin shirye-shiryen Sallah.
Mutane da dama kan yi sayayya, su shirya ziyartar iyalai, sannan su bayar da zakka ta musamman wato Zakatul Fitr kafin a gudanar da sallar Idi.
Sanarwar hutun tun da wuri ta bai wa ma’aikata da kamfanoni damar tsara tafiya, kasuwanci da bukukuwan Eid al‑Fitr cikin kwanciyar hankali.
Rikicin Gabas ta Tsakiya zai iya shafar hajji
Tun farko, an ji cewa rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila na iya jawo cikas ga tafiyar maniyyatan Umrah daga Najeriya.
Rufe wasu filayen jirgin sama a Gabas ta Tsakiya ya haddasa rudani da fargaba ga masu shirin zuwa Saudiyya.
Duk da cewa Saudiyya ba ta rufe filayen jiragen sama ba, ana tsoron hare-haren za su iya shafar jigilar maniyyata.
Asali: Legit.ng

