Isra’ila Ta Sake Kai Hari Lebanon, Ta Farmaki Manyan Jami’an Rundunar Iran

Isra’ila Ta Sake Kai Hari Lebanon, Ta Farmaki Manyan Jami’an Rundunar Iran

  • Isra’ila ta sake kaddamar da hare-hare a kudancin Lebanon, inda ta nufi wasu manyan jami’an rundunar Quds ta Iran
  • Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi alkawarin za a ga “abubuwan mamaki da dama” a sabon matakin yakin
  • Hare-haren sun zo ne bayan Isra’ila ta kai farmaki kan wani wurin ajiyar mai a Tehran ranar Asabar 7 ga watan Maris

Beirut, Lebanon — Isra’ila ta sake kaddamar da hare-hare a kudancin Lebanon da safiyar ranar Lahadi, 8 ga Maris, inda ta nufi wasu kwamandojin bangaren Lebanon na rundunar Quds ta dakarun juyin juya halin Iran.

Wannan mataki ya biyo bayan furucin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, wanda ya yi alkawarin cewa za a ga “abubuwan mamaki da dama” a mataki na gaba na yakin da ke gudana tsakanin Iran da Amurka/Isra’ila.

Sojojin Isra’ila sun bayyana a cikin wata sanarwa cewa ba za su bari “kungiyoyin ta’addanci na Iran su kafa sansani a cikin kasar Lebanon ba.”

Kara karanta wannan

Kasar Muslunci ta Iran ta nuna sha'awar taimakawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci

Isra'ila ta sake farmakar Lebanon
Sojin Isra'ila sun farmaki Lebanon | @HarmlessHQ
Source: Twitter

Harin wurin ajiyar mai a Tehran

Sabbin hare-haren a Lebanon sun biyo bayan wani farmaki da Isra’ila ta kai ranar Asabar, 7 ga Maris, kan wani wurin ajiyar mai a Tehran.

Rahotanni sun nuna cewa wutar da ta tashi daga wurin ta shafi manyan ginshikan wuta da kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya wallafa, inda hasken wutar ya bayyana a sararin sama da dare.

Ana ganin wannan ne karo na farko da aka kai hari kan wata cibiyar masana’antu ta farar hula tun bayan barkewar wannan yaki.

Kafafen yada labaran gwamnatin Iran sun zargi Amurka da Isra’ila da kai wannan hari a wurin da ke samar da man fetur ga birnin Tehran da wasu larduna da ke arewacin kasar.

Mutane sun mutu a Lebanon da Kuwait

A wani bangaren kuma, hukumomin Kuwait sun ce jami’an tsaron iyaka biyu sun mutu bayan wani hari da aka kai da makamai masu linzami da jirage marasa matuka a kasar.

Kara karanta wannan

Iran ta kada hantar Isra'ila, ta fadi tsawon lokacin da za ta yi tana yakarta

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Kuwait ta ce jami’an sun mutu ne “yayin da suke gudanar da aikin kasa,” amma ba ta bayar da karin bayani ba a kansu.

Kuwait na daga kasashen da ke zagaye da Iran, kuma suke da sansanonin sojin Amurka a cikinsu, lamarin da ya sa Iran ke farmakar kasar.

Mutanen da aka kasha a Lebanon

A Lebanon kuwa, ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce hare-haren sama na Isra’ila sun kashe mutane takwas a kudancin kasar.

Rahotannin kafafen yada labarai na cikin gida sun kuma bayyana cewa wani jirgin yaki maras matuki na Isra’ila ya kai hari kan wani otel a birnin Beirut, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu goma.

Wadannan mace-mace sun kara adadin wadanda suka rasa rayukansu bayan akalla mutane 47 da suka mutu a hare-haren Isra’ila da aka kai ranar Asabar.

An kashe shugaban Hezbollah a Lebanon

A wani harin da sojin Isra’ila suka kai a 2024 a birnin Beirut, sun hallaka shugaban dakarun Hezbollah, Hassan Nasrallah.

Wannan na zuwa ne daga wata majiya da jami’in da ya shaidawa CBS, kamar yadda BBC ta tattaro.

Sai dai, wani rahoton ya bayyana cewa, shugabannin sojin Isra’ila sun ce batun ya yi wuri a bayyana ko Nasrallah ya kwanta dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng