Bayan babban fashewar watan jiya, gobara ta sake kamawa a birnin Beirut, kasar Lebanon (Hotuna da Bidiyo)

Bayan babban fashewar watan jiya, gobara ta sake kamawa a birnin Beirut, kasar Lebanon (Hotuna da Bidiyo)

Ana gobara yanzu haka a tashar ruwan Beirut, babbar birnin kasar Lebanon, yan makonni bayan mumunar tashin sinadarin Bam, Ammonium Nitrate, da yayi sababin asarar rayuka da dukiya.

Za ku tuna cewa a ranar 4 ga agusta, 2020, kimanin mutane 191 suka rasa rayukansu kuma daruruwa suka jikkata yayinda ton 2,750 na Ammonium Nitrate da aka ajiye a tashar ruwa ya fashe.

A yanzu wuta ta kama wani dakin ajiya a cikin daya daga wuraren da suka kone a baya.

Bidiyoyin gobaran sun nuna yadda wuta ke ci bal-bal,

Har yanzu ba'a san abinda ya sabbaba gobarar ba.

Kalli hotuna da bidiyo:

Bayan babban fashewar kwanaki, gobara ta sake kamawa a birnin Beirut, kasar Lebanon (Hotuna da Bidiyo)
Bayan babban fashewar kwanaki, gobara ta sake kamawa a birnin Beirut, kasar Lebanon (Hotuna da Bidiyo)
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Mun ceto mutane 5 cikin wadanda aka sace a Abuja cikin daren Laraba - Yan sanda

Bayan babban fashewar kwanaki, gobara ta sake kamawa a birnin Beirut, kasar Lebanon (Hotuna da Bidiyo)
Bayan babban fashewar kwanaki, gobara ta sake kamawa a birnin Beirut, kasar Lebanon (Hotuna da Bidiyo)
Source: Twitter

Bayan babban fashewar kwanaki, gobara ta sake kamawa a birnin Beirut, kasar Lebanon (Hotuna da Bidiyo)
Bayan babban fashewar kwanaki, gobara ta sake kamawa a birnin Beirut, kasar Lebanon (Hotuna da Bidiyo)
Source: Twitter

Manyan abubuwan fashewa tamkar bama-bamai biyu sun rikita babbar birnin Lebanon, Beirut ranar Talata, 4 ga Agusta, inda dimbin mutane suka rasa rayukansu kuma da dama sun jikkata.

Wani rahoton BBC ya bayyana cewa shugaban harkokin tsaron cikin gidan kasar ya ce Bama-baman sun tashi ne a unguwar da akayi ajiyar kaya masu iya tashin Bam.

Tuni dai Firam Ministan kasar, Hasan Diab, ya alanta ranar Laraba matsayin ranar makoki.

Ministan lafiyar kasar, Hamad Hassan ya ce kimanin mutane 2,500 sun jikkata.

Ga jerin abubuwa 5 da muka sani kawo yanzu:

1. Akalla asibitoci uku sun kone kurmus

2. Akalla mutane 100 sun mutu kuma akalla 2,500 sun jikkata, cewar ministan lafiya

3. Akwai yan kasar Phillippines biyu da dan kasar Australiya daya cikin mamata

4. Kasashen Iran, Cyprus, da Malaysiya sun bayyana niyyar taimako

5. An gano sinadarin Ammonium nitrate NH4NO3 ne ya sabbaba fashewar

6. An ajiye Ammonium nitrate NH4NO3 a tashar ruwan ne tun shekarar 2013

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel