Ana Tsakiyar Musayar Wuta, An Zabi Wanda Zai Zama Sabon Jagoran Addini a Iran

Ana Tsakiyar Musayar Wuta, An Zabi Wanda Zai Zama Sabon Jagoran Addini a Iran

  • Wasu daga cikin mambobin Majalisar kwararru da ke da alhakin zaben sabon jagoran addinin Iran sun tabbatar da cewa an gama kada kuri'a
  • A cewarsu, sun riga sun zabi sabon jagoran addinin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda zai gaji marigayi Ayatollahi Ali Khamenei
  • Mohsen Heydari, wanda ke wakiltar lardin Khuzestan a majalisar, ya ce an riga an zabi wanda ya fi dacewa da mukamin jagoran Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Majalisar malaman addini da ke da alhakin zaben sabon jagoran addini na Iran ta bayyana cewa ta riga ta cimma matsaya kan wanda zai gaji marigayi Ali Khamenei.

Sai dai har kawo yanzu Majalisar ba ta fito ta bayyana sunansa a hukumance ba tukuna, wanda ake zargin jinkirin yana da alaka da yakin da Iran ke yi da Amurka/Isra'ila.

Kara karanta wannan

Iran ta yi wa Trump martani daga Najeriya kan maye gurbin Ayatollah Khamenei

Ali Khamenei.
Tsohon jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Twitter

An zabi sabon jagoran kasar Iran

The Times of Israel ta tattaro cewa Ahmad Alamolhoda, daya daga cikin mambobin Majalisar Kwararru ta Iran, ya ce an riga an gudanar da kuri’ar zaben sabon jagoran.

“An kada kuri’ar zaben jagora kuma an zabi wanda zai jagoranci kasar,” in ji Alamolhoda.

Ya kara da cewa hedkwatar majalisar za ta sanar da sunan sabon jagoran kasar Iran nan gaba kadan. Ana zargin Mojtaba Khamenei na iya zama magajin mahaifinsa.

Wanda ake tunanin zai zama jagoran Iran

Wasu mambobin majalisar sun tabbatar da cewa an cimma matsaya, inda daya daga cikinsu ya nuna yiwuwar cewa Mojtaba Khamenei, dan marigayi Ali Khamenei, ne zai gaji mahaifinsa.

Tun da dadewa ake hasashen Mojtaba zai iya zama magajin mahaifinsa, wanda ya zama jagoran addini na Iran tun shekara ta 1989.

Matsayin jagoran addini shi ne mafi girman iko na siyasa da addini a Iran, kuma shi ke da ikon yanke hukunci na karshe kan manyan al’amuran kasa.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani kan jita jitar kashe wanda ake sa ran zai gaji Khamenei a Iran

Mohsen Heydari, wanda ke wakiltar lardin Khuzestan a majalisar, ya ce an riga an zabi wanda ya fi dacewa da mukamin jagoran Iran.

“Muna da tabbacin cewa an zabi wanda ya fi dacewa, wanda mafi yawan mambobin majalisar suka amince da shi,” in ji shi.
Mojtaba Khamenei.
Mojtaba Khamenei, dan marigayi jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei Hoto: Forrest Anderson
Source: Getty Images

Martani kan maganar Trump

A bangare guda kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana son taka rawa wajen zaben sabon jagoran Iran, tare da kin amincewa da yiwuwar cewa Mojtaba Khamenei zai gaji mahaifinsa, yana mai kiransa da “mutum mara karfi.”

Sai dai jami’an gwamnatin Iran sun yi watsi da wannan magana, suna jaddada cewa Amurka ba ta da ikon sa hannu a zaben sabon jagoran kasar, cewar jaridar Arab News.

Iran ta ruguza lissafin kasar Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta bayyana cewa Amurka ta yi tunanin za ta kai mata farmaki kuma cikin kankanin lokaci za ta murkushe ta amma sai ta ga akasin haka.

Babban sakataren majalisar tsaron ƙasa ta Iran , Ali Larijani, ya bayyana cewa Amurka ta yi zaton cewa bugu daya za ta yi wa Iran ta samu nasara a kanta musamman idan ta kashe Khamenei.

A cewarsa, duk da hare-haren hadin gwiwa da kasashen Isra'ila da Amurka suka kai, al’ummar Iran sun hada kai wajen kare kasarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262