Lamari Ya Rincabe: Saudiyya Ta Gaji da Shiru, Ta Gargadi Iran kan Hare Harenta

Lamari Ya Rincabe: Saudiyya Ta Gaji da Shiru, Ta Gargadi Iran kan Hare Harenta

  • Kasar Saudiyya ta tura gargadimai zafi ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran game da hare-hare a kasarta a yakin da ake yi
  • Saudiyya ta gargadi Iran kada ta kai hari kan kasarta, tare da yi mata kashedin yiwuwar mayar da martani idan harin ya ci gaba
  • Ministan harkokin wajen Saudiyya, Faisal bin Farhan, ya tattauna da takwaransa na Iran, Abbas Araqchi, kan bukatar rage tashin hankali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyadh, Saudiyya - Rahotanni sun nuna cewa Saudiyya ta tura gargadi mai tsauri ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan yakin da ake yi.

Saudiyya ta ce duk wani hari da zai ci gaba kan masarautar ko bangaren makamashinta na iya tilasta mata mayar da martani.

Saudiyya ta tura gargadi ga Iran
Marigayi Ali Khamenei da Dan Sarkin Saudiyya, Muhammad Bn Salman. Hoto: @khamenei_ir, Inside the Haramain.
Source: Twitter

Jawabin shugaban Iran ga kasashen Larabawa

Majiyoyi hudu da suka san yadda lamarin ya faru sun shaida wa Reuters cewa an isar da wannan sako ga Tehran kafin wani jawabi da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya gabatar.

Kara karanta wannan

Iran ta gamu da gagarumar matsala tana tsakiyar musayar wuta da Amurka/Isra'ila

Pezeshkian ya nemi afuwa ga kasashen makwabta na yankin Gulf kan matakan da Iran ta dauka.

An ce wannan mataki na neman afuwar wani kokari ne na rage fushin kasashen yankin bayan hare-haren Iran da suka taba wasu wuraren fararen hula.

Matsayar Saudiyya kan hare-haren Iran a kasar

Kwana biyu kafin haka, ministan harkokin wajen Saudiyya, Faisal bin Farhan, ya tattauna da takwaransa na Iran, Abbas Araqchi, inda ya bayyana matsayar Riyadh a fili.

Majiyoyin sun ce Saudiyya ta bayyana cewa tana bude kofa ga duk wata shiga tsakani da za ta taimaka wajen rage tashin hankali da kuma samar da sulhu ta hanyar tattaunawa.

Ministan ya ce idan hare-haren Iran kan yankin Saudiyya suka ci gaba, za ta iya ba sojojin Amurka damar amfani da sansanoninsu da ke cikin kasar domin gudanar da ayyukan soja.

Har ila yau, Riyadh za ta mayar da martani idan hare-haren kan muhimman cibiyoyin makamashi na kasar suka ci gaba, cewar Times of Israel.

Saudiyya ta sha alwashin daukar fansa kan hare-hare
Dan Sarkin Saudiyya, Yarima Muhammad Bin Salman. Hoto: Inside the Haramain.
Source: Facebook

Yadda Saudiyya ta ke tuntubar Iran

Kara karanta wannan

Ba sauki: Iran ta kai hari mai zafi kan sansanin sojojin Amurka

Majiyoyin sun kara da cewa Saudiyya ta ci gaba da tuntubar Tehran ta hannun jakadanta tun bayan da yakin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila kan Iran ya fara a ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan rushewar tattaunawar shirin nukiliyar Iran.

Kasashen yankin Gulf da suka hada da United Arab Emirates, Kuwait, Qatar, Bahrain da Saudi Arabia sun fuskanci hare-haren jiragen yaki marasa matuki da makamai masu linzami daga Iran a cikin makon da ya gabata.

A cikin wata hira, Araqchi ya ce yana ci gaba da tuntuba da ministan harkokin wajen Saudiyya da sauran jami’an kasar, inda Riyadh ta tabbatar masa cewa ba za ta bari a yi amfani da kasarta, ruwanta ko sararin samaniyarta wajen kai hari kan Iran ba.

Shugaban Iran, Pezeshkian, ya kuma ce majalisar wucin gadi da ke jagorantar kasar ta amince da dakatar da hare-hare kan kasashen makwabta, sai dai idan har wani hari kan Iran ya fito daga wadannan kasashe.

Ya ce:

“Ni da kaina ina neman afuwa daga kasashen makwabta da matakan Iran suka shafa.”

Saudiyya yana neman agaji kan yakin Iran/Isra'ila

An ji cewa ma'aikatar tsaron Saudiyya ta gana da shugaban sojojin Pakistan game da wata jarjejeniyar da kasashen suka kulla a shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta shiga duniya neman kariya daga hare haren Iran

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da gwabza yakin Iran da Amurka/Isra'ila da ya shafi kasashe da dama a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ministan tsaron Saudiyya, Yarima Khalid bin Salman, ya yi magana game da fargabar yaduwar yakin zuwa kasashen da ba da su ake yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.