Yaki na Kara Zafi, Trump Ya Ja da Baya, Ya Ki Tura Sojoji Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ba zai tura sojoji Iran ba bayan kaddamar da hare-haren soji ta sama a kasar
- Trump ya bayyana haka ne yayin wasu tambayoyi da aka masa game da matakan da zai dauka domin ganin samun nasara a Iran
- Yayin da aka shiga kwana na bakwai na yakin, dukkan bangarorin na nuna cewa su ne suke da nassara kuma babu maganar tsagaita wuta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Iran da Amurka/Isra'ila na cigaba da kai hare-hare ga juna bayan yakin da ya barke a tsakaninsu tun ranar Asabar, 28 ga Maris, 2026.
Yayin da ya ke amsa tambayoyi game da yakin da ake gwabzawa, shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ba zai tura sojojin Amurka Iran ba.

Source: Getty Images
Rahoton tashar France 24 ya nuna cewa Donald Trump ya fadi dalilan da za su hana shi daukar matakin tura sojojin Amurka zuwa kasar Iran.
Maganar Donald Trump kan tura sojoji Iran
Donald Trump ya ce Amurka ba ta tunanin tura dakarun sojojin ƙasa cikin Iran a yanzu, yana mai cewa hakan zai zama ɓata lokaci.
Trump ya kuma yi watsi da gargadin ministan harkokin wajen Iran cewa matakin zai zama bala’i ga duk sojan da ya kuskura aka tura shi.
Trump ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta waya da NBC, inda ya ce:
“Ba shi da amfani a yanzu. Sun riga sun rasa komai. Sun rasa rundunar ruwansu. Sun rasa duk abin da ya kamata su rasa.”
Ya ƙara da cewa kalaman Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi cewa Iran a shirye take don kakkabe masu mamaya daga Amurka ko Isra’ila, inda ya ce:
“Magana ce marar amfani.”

Source: Twitter
Maganar zaben sabon Shugaban Iran
Game da wanda zai maye gurbin Ayatollah Khamenei, Trump ya kuma nuna cewa yana sha’awar ganin an sauya tsarin jagorancin Iran, yana mai cewa:
“Muna son mu shiga mu sauya komai cikin gaggawa.”
TRT World ta rahoto ya ƙara da cewa Amurka ba ta son wani shugaba da zai sake gina tsarin kasar cikin shekaru 10 ya samu ragamar jagoranci a yanzu.
“Muna da wasu ra’ayoyi kan wanda zai zamo sabon shugaba a kasar,”
Inji shi, amma ya ƙi bayyana sunan duk wanda yake so.
A baya Trump ya ce dole ne ya kasance cikin masu ruwa da tsaki wajen naɗa sabon shugaban Iran, bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai suka kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Kurdawa sun ki taimakon Trump
A wani labarin, kun ji cewa matar shugaban kasar Iraq, Shanaz Ibrahim Ahmed ta ce Kurdawa ba za su shiga yakin da Amurka ke yi da Iran ba.
Ta bayyana haka ne yayin wani taron tunawa da Kurdawa da suka rasu a yake-yake da gwagwarmayar da suka yi a shekarun baya.
Matar shugaban kasar ta bayyana cewa a baya an yaudare su a wani yaki da aka yi a lokacin Saddam Hussain da kuma kasar Syria.
Asali: Legit.ng


