Iran Ta Harba Makamai Masu Linzami kan Babban Birnin Isra'ila, an Ji Barnar da Suka Yi
- Ana ci gaba da gwabza fada mai zafi tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Oran a yankin Gabas ta Tsakiya
- Kasar Iran ta harba wasu makamai masu linzami zuwa birnin Tel-Aviv na Isra'ila yayin da ake ci gaba da kai hare-hare
- Masu kashe gobara sun garzaya wuraren da makaman suka sauka a cikin babban birnin domin kashe wutar da ta tashi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv - Sabon luguden wuta na makamai masu linzami da Iran ta harba ya haddasa jerin fashe-fashe a fadin birnin Tel Aviv.
Ma'aikatan kwana-kwana sun dukufa wajen kashe wata gobara da ta tashi a wani gini kusa da babbar cibiyar kasuwancin Isra'ila.

Source: Twitter
Jaridar The Hindu ta ce AFP ta kawo rahoton cewa Iran ta harba makaman ne masu linzami a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris 2026.
Ana kai hare-hare a Gabas ta Tsakiya
Wadannan hare-hare sun biyo bayan fadada farmakin da Isra'ila ke kai wa kungiyar Hezbollah, inda ta lashi takobin daukar fansa kan kungiyar mayakan da Iran ke marawa baya.
Isra'ila ta lashi takobin farmakar Hezbollah ne saboda shigar ta cikin rikicin bayan kisan jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a ranar Asabar.
Iran ta harba makamai kan Isra'ila
The Punch ta ce gidan rediyo da talabijin na gwamnatin Iran ya bayyana cewa Tehran ta harba makaman ne "kan wasu wurare da ke tsakiyar Tel Aviv,"bayan da dakarun sojojin Isra'ila suka ce suna kokarin kakkabo makaman da Iran ta harbo a daren ranar Alhamis.
Rahotanni sun ce a birnin Tel Aviv an ji jerin fashe-fashe guda biyu a lokaci guda da suka girgiza birnin baki daya.
Haka kuma, hasken makaman ya mamaye sararin samaniyar Netanya, wani birni da ke Arewacin Tel Aviv a gabar tekun Bahar Rum.
Isra'ila ta yi kokarin kashe wuta
Bayan harin, hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra'ila, Magen David Adom (MDA), ta bayyana cewa dakarunta sun ziyarci wurare da dama da makaman suka fada, amma babu rahoton asarar rayuka.
Rundunar 'yan sandan Isra'ila ta ce "a halin yanzu tana binciken wuraren da ragowar makaman suka fada a tsakiyar Isra'ila," inda ta kara da cewa akwai "lalacewar dukiya" amma babu mutanen da suka jikkata.

Source: Twitter
Wani makami ya fada kan wani gini a gefen birnin Tel Aviv, wanda hakan ya tilasta wa mazauna ginin ficewa domin tsira da rayukansu.
A wani ginin kuma kusa da cibiyar tattalin arzikin kasar, ma'aikatan kashe gobara sun yi kokarin kashe wutar da ragowar makamin da aka kakkabo ya haddasa.
Hukumar tsaron gida ta Isra'ila ta fitar da gargadin harba makamai da dama a safiyar ranar Juma'a ga al'ummomin da ke kusa da iyakar kasar da Lebanon.
Isra'ila ta fadi dalilin kashe Khamenei
A wani labarin kuma, kun ji cewa Isra'ila ta yi magana kan kisan da dakarunta suka yi wa jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Kakakin rundunar sojojin Isra'ila ya bayyana cewa kisan da aka yi wa Khamenei bai sabawa dokokin kasa da ksa kan yaki ba.
Nadav Shoshani ya bayyana cewa kasancewar Khamenei a matsayin babban kwamandan sojojin Iran, ya sanya zama halastaccen wanda za a iya kai wa farmaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

