Lissafi zai Kwabewa Trump, Mayakan Kurdawa Sun Ki Taya Shi Yaki da Iran

Lissafi zai Kwabewa Trump, Mayakan Kurdawa Sun Ki Taya Shi Yaki da Iran

  • Kurdawan Iraq sun yi watsi da bukatar shugaban Amurka da ke neman su taya shi yaki da kasar Iran wajen kai hari Tehran a gwabzawan da ake
  • Rahoto ya ce Shugaba Donald Trump ya nemi Kurdawa su taya shi fada ne maimakon tura sojojin Amurka su fafata da dakarun Tehran ta kasa
  • Amurka da Isra'ila sun hada kai sun kai hari Iran a ranar Asabar, 28 ga Fabrairun 2026, lamarin da ya jawo mutuwar jagoran addini, Ayatollah Ali Khamenei

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iraq - Uwargidan shugaban kasar Iraq, Shanaz Ibrahim Ahmed, ta bukaci Amurka da ta daina kallon Kurdawa a matsayin 'yan haya a yaƙin da ake yi da Iran.

Ta bayyana haka ne a daidai lokacin da ake zargin akwai wani shiri na Amurka da Isra’ila na jawo dakarun Kurdawa cikin yaƙi da Tehran.

Kara karanta wannan

Iran ta ce ta kashe sojojin Amurka 500 a luguden wuta da ta masu

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sakon da ta wallafa a X ya nuna cewa ta bayyana haka ne a lokacin cika shekaru 35 da tayar da ƙayar baya ta Kurdawa a shekarar 1991 kan mulkin Saddam Hussein.

Iran: Martanin Kurdawa ga Donald Trump

Shanaz Ibrahim Ahmed wacce fitacciyar jagora ce a cikin Kurdawa kuma matar shugaban ƙasar Iraq, Abdul Latif Rashid, ta yi amfani da darussan tarihi domin ƙarfafa saƙonta ga Trump.

Ta ce ta tuno da tayar da ƙayar bayan da ta faru a Sulaymaniyah, lokacin da Kurdawa suka tashi tsaye kan Saddam a 1991, amma daga baya aka murkushe su.

“Babu wanda ya zo ya kare mu,”

Inji ta a cikin sanarwar, tana mai jaddada cewa wadannan abubuwa har yanzu suna nan a cikin zukatan Kurdawa kuma ba su manta da su ba.

Ta bayyana wannan babi na tarihi a matsayin darasi da bai kamata a manta da shi ba, tare da kira ga kowa da kowa da kada a sake maimaita irin wannan cin amana.

Kara karanta wannan

Yakin Amurka/Isra'ila da Iran: Muhimman abubuwan da suka faru a rana ta 5

Halin da Kurdawa suka shiga a Syria

Da ta juya zuwa batutuwan da ke faruwa a yanzu, Shanaz ta yi nuni da abubuwan da suka faru a Arewa maso Gabashin Syria, yankin da ake kira Rojava.

Ta ce Kurdawan Syria ne suka yi yaƙi da mayaƙan Daesh, amma daga baya suka fuskanci watsi duk da alkawuran goyon baya da aka yi musu.

Tashar Press TV ta rahoto Shanaz ta ce:

“An yi alƙawura, bayan Kurdawan Syria sun tsaya a sahun gaba wajen yaƙi da ISIS, mun ga yadda aka yi mu’amala da su.”
Shanaz Ibrahim Ahmad
Matar shugaban ƙasar Iraq, Shanaz Ibrahim Ahmad. Hoto: @firstladyofiraq
Source: Twitter

A cewar wasu majiyoyi da dama, hukumar leƙen asirin Amurka (CIA) na aiki domin samar wa ƙungiyoyin mayaƙan Kurdawa da ke Arewacin Iraq makamai.

Trump zai kai farmaki ƙasar Cuba

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya sake yi wa kasar Cuba barazana yayin wani taro a fadar White House.

Kara karanta wannan

Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

Donald Trump ya nuna cewa zai kai farmaki ƙasar Cuba da shirin kifar da gwamnati idan ya kammala yaƙin da ya fara da Iran.

Tun a baya dai Trump ya sanya wa Cuba takunkumi, musamman game da man fetur bayan kama shugaban ƙasar Venezuela.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng