Babbar Magana: Ana cikin Yaki da Iran, Tsohon Soja Ya Tayar da Tarnaki a Majalisar Amurka

Babbar Magana: Ana cikin Yaki da Iran, Tsohon Soja Ya Tayar da Tarnaki a Majalisar Amurka

  • Wani tsohon soja a Amurka ya shiga wani zama da ake yi na kwamitin majalisar dattawa kan abin da ya shafi tsaro
  • Tsohon sojan wanda yake dan takarar kujerar sanata ne ya gayawa mutanen da ke wajen matsayarsa kan yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran
  • Jami'an 'yan sanda sun yi amfani da karfi wajen fitar da tsohon sojan daga zaman da ake yi, inda suka samu taimako daga wajen wani sanata

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Amurka - Wani tsohon sojan Amurka ya tayar da bore yayin zaman wani kwamitin majalisar dattawa.

Sanata Tim Sheehy na jam'iyyar Republican daga jihar Montana, ya taimaka wa jami'an 'yan sanda da dama wajen fitar da mutumin, wanda ya katse zaman da ake yi a Capitol Hill domin nuna rashin amincewa da yaƙin Amurka da Isra’ila da ƙasar Iran.

Kara karanta wannan

An ci mutuncin dan takarar sanata da ya soki Amurka saboda hari kan Iran

Tsohon soja ya tayar da rigima a majalisar Amurka
Sanatoci yayin zama a majalisar dattawan Amurka Hoto: Daniel Barry
Source: Getty Images

Tashar CBS News ta kawo rahoton cewa lamarin ya auku ne a ranar Laraba, 4 ga watan Maris, 2026.

Tsohon soja ya yi adawa da yakin Iran

Mai zanga-zangar nuna adawa da yaki da Iran shi ne Brian McGinnis, wani tsohon soja wanda ke takarar neman kujerar Sanata a jihar North Carolina a ƙarƙashin jam'iyyar Green Party.

Jim kaɗan bayan faruwar lamarin, McGinnis ya bayyana cewa hannunsa ya karye yayin karawar da aka yi da 'yan sanda da kuma sanatan.

Sai dai rundunar 'yan sandan Capitol ta Amurka ta zarge shi da kai "mummunan hari" ga jami'an tsaro.

Lamarin ya faru ne a wani zama na ƙaramin kwamitin ayyukan sojoji na majalisar dattawa, inda manyan jami'an soja suke bayar da shaida kan shirye-shiryen yaƙi na dakarun sojoji.

Tsohon soja ya tayar da bore a majalisa

Ƙasa da mintuna 30 bayan fara zaman, McGinnis ya fara magana, inda a wani lokaci yake cewa: "Amurka ba ta son tura 'ya'yanta maza da mata zuwa yaƙi saboda Isra'ila."

Kara karanta wannan

Sanatocin Amurka sun kada kuri'a kan hana Trump cigaba da yaki da Iran

Jami'an 'yan sandan Capitol sun yi ƙoƙarin fitar da McGinnis wanda yake sanye da kakin soja daga ɗakin taron.

A lokacin da McGinnis da 'yan sanda suke kusa da ƙofar fita daga ɗakin taron, Sanata Sheehy ya bar wurin zamansa ya fara taimaka wa jami'an 'yan sandan wajen ɗaga shi da kuma tura shi waje.

Yayin da hukumomi suke ƙoƙarin fizge McGinnis daga ɗakin, hannunsa na hagu ya maƙale a tsakanin ƙofa da jikin bangon ƙofar.

A lokacin ne aka ga Sheehy yana ƙoƙarin cire hannun, inda a nan ne wani ya zargi sanatan da karya wa McGinnis hannu.

Wani ya tambayi McGinnis ko hannunsa yana lafiya, sai ya amsa da cewa, "A'a, ba lafiya kalau yake ba."

Tsohon sanata ya tayar da bore a majalisar Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J. Trump
Source: Facebook

An karya hannun tsohon sojan Amurka

Daga baya 'yan sanda suka raka McGinnis zuwa waje yayin da Sanata Sheehy ya koma ya zauna. A lokacin da yake wajen ɗakin, an ji McGinnis a cikin bidiyo da @alanhe ya sanya a shafinsa na X yana cewa hannunsa na hagu ya karye.

Kara karanta wannan

Asara ta fara bin Amurka, ta rasa biliyoyin Daloli kwanaki 5 da fara yakin Iran

Mark Elbourno, wani jami'in jam'iyyar Green Party wanda ke kula da kamfen ɗin McGinnis, ya bayyana cewa an kama McGinnis kuma an kai shi asibitin jami'ar George Washington.

Elbourno ya ce ba shi da tabbas kan yanayin lafiyar McGinnis a halin yanzu.

Sanata ya yi magana kan lamarin

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Sheehy ya bayyana cewa ya sa baki ne saboda McGinnis ya riƙa “fafatawa” da jami’an yan sanda, don haka ya yi ƙoƙarin ba da taimako domin kwantar da tarzomar.

“Wannan mutumin ya zo majalisa ne (da nufin neman rigima, kuma ya same ta. Ina fatan zai sami taimakon da yake buƙata ba tare da ya sake janyo wani tashin hankalin ba.”

- Tim Sheehy

Amurka ta rufe ofishinta a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ofishin jakadancin Amurka a Najeriya da ke birnin tarayya Abuja ya sanar da dakatar da aiki saboda wata barazana da ya hango a kasar.

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da dakatar da aiki saboda yiwuwar zanga-zangar da za ta iya jawo tashin hankali.

Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin kasashen Amurka, Isra'ila da Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng