Faransa Ta Ja Kunnen Netanyahu yayin da ake Gwabza Yakin Iran da Amurka
- Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya gargadi Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu game da kai hari yankunan Lebanon
- Hakan na zuwa ne bayan 'yan Hezbullah da ke Lebanon sun kai hare-hare kan Isra'ila yayin da ke cigaba da gwabza yakin kasar Iran da Amuka
- Shugaba Macron ya bayyana cewa yana tare da mutanen da aka riga aka raba da gidajensu a Lebanon, inda ya ce za su kai musu tallafi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Faransa - Faransa ta yunkuro domin tsayar da wutar rikici da ta kunno kai tsakanin Isra'ila da Lebanon bayan fara kai hari yankunan Tel Aviv.
Lamari ya zafafa ne a lokacin da 'yan Hezbullah suka kai hare-hare Isra'ila da sunan taya Iran yaki da Amurka a rikicin da ya barke a Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Kasar Faransa ta gargadi Benjamin Netanyahu
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya wallafa a X cewa ya kira Benjamin Netanyahu ta wayar tarho ya yi masa gargadi game da rikicin.
Macron ya ce:
"Na yi tattaunawa a yau da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, tare da Shugaban Jamhuriyar Lebanon Joseph Aoun da kuma Firaminista Nawaf Salam, domin tattauna halin da ake ciki a Lebanon wanda ke matuƙar tayar da hankali."
"Haka kuma na gargadi Firaministan Isra’ila da ya mutunta cikakken ikon ƙasar Lebanon kan yankinta tare da gujewa kai farmakin sojoji ta ƙasa. Yana da muhimmanci bangarorin su koma ga yarjejeniyar tsagaita wuta."

Source: Getty Images
Makomar alakar Faransa da Lebanon
Macron ya ce Faransa za ta ci gaba wajen tallafa wa rundunar sojojin Lebanon domin su iya aikinsu na kare ikon ƙasar da kuma kawo ƙarshen barazanar da Hezbollah ke haifarwa.
Dangane da matsalar jin-ƙai da ta taso a kudancin Lebanon, Faransa ta ce za ta ɗauki matakan gaggawa domin tallafa wa ‘yan ƙasar Lebanon da suka rasa muhallansu.
Macron ya ce:
"Goyon bayanmu ga al’ummar Lebanon da kuma jajircewarmu wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin na ci gaba da kasancewa ginshiƙi a cikin ayyukanmu."
Hezbullah ta kai hari Isra'ila
Al-Jazeera ta rahoto cewa kungiyar Hezbullah ta bayyana cewa tana cigaba da kai hare-hare 'yankunan Isra'ila a yakin da ake cigaba da yi a yankunan Gabas ta tsakiya.
A ranar Laraba, 5 ga watan Maris, 'yan Hezbullah sun bayyana cewa su suka kai hari da rokoki kan sojojin Isra'la a yankin Metula da makamai masu linzami a Haifa.
Faransa ta tura jirage Gabas ta Tsakiya
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Faransa ta sanar da tura jiragen yaki kasashen Larabawa yayin da ake cigaba da yakin Iran da Amurka/Isra'ila.
Sai dai ta sanar da cewa ba yaki da Iran jiragen za su shiga ba, za su rika shawagi a sama ne domin kare sansanin sojojin Faransa a yankin.
Kamar Amurka, Faransa na da sansanin soji a yankunan Gabas ta Tsakiya, inda ta ke kokarin tabbatar da babu abin da ya same su a yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

