Kanada Ta Gano Masu Laifi a Yakin da Ya Barke tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran

Kanada Ta Gano Masu Laifi a Yakin da Ya Barke tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran

  • Kasar Kanada ta tsoma baki kan yakin da ya barke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Amurka da Isra'ila
  • Firaministan Kanada, Mark Carney ya ce hare-haren da Amurka da Isra'ila suka fara kai wa Iran ya saba wa dokokin kasa da kasa
  • Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga rana ta biyar da fara musayar wuta tsakanin kasashen, lamarin da ya jawo asarar rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Canada - Firaministan Canada, Mark Carney, ya bayyana cewa hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran ya saba wa dokar kasa da kasa ta duniya.

Carney ya yi wannan bayani ne yayin wani taro da Lowy Institute ta shirya a birnin Sydney na kasar Australia.

Mark Carney.
Firaministan Kanada, Mark Carney a taron da ya halarta a kasar Australia Hoto: Ayush Kumar
Source: Getty Images

A rahoton da Leadership ta kawo, Firaministan ya ce Kanada na maraba da duk wani yunkuri da zai kawo sauyi a tsarin mulkin Iran, wanda ya bayyana a matsayin tushen rashin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Luguden wutar Iran ya jefa Amurkawa cikin tsoro, suna korafi ga Trump

Kanada ta yi magana kan yakin Iran

Sai dai ya ce duk da Kanada na son a samu sauyin gwamnati a Iran, amma a zahiri hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai mata ba su yi daidai da ka’idojin dokokin kasa da kasa ba.

“A ganina, abin bai da alaka da dokokin kasa da kasa, amma hukuncin karshe na hannun kwararrun masana. Ni ba lauya ba ne, balle kuma kwararre a dokokin kasa da kasa.”

Wannan furuci nasa ya zo ne a rana ta biyu na ziyararsa a Australia, a wani bangare na rangadin yankin Asia-Pacific domin jawo zuba jari da kuma karfafa alaka da kasashen da ake kira masu matsakaicin karfi.

Ya ce rangadin na da nufin rage dogaro da Amurka, musamman yayin da yake gargadin cewa tsarin duniya da Amurka ke jagoranta na fuskantar rauni.

Abin da ya hada Kanada da Shugaba Trump

Carney, ya sha yin sukar Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya taba yin barazanar hade Canada da Amurka tare da kakaba wa kayayyakin Kanada haraji mai tsanani.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta fadi wani babba da ta ke shirin hallaka wa a kasar Iran

A ranar Laraba, ya bayyana rikicin Gabas ta Tsakiya a matsayin wani misali na gazawar tsarin kasa da kasa, yana mai sake kira ga kaasashen duniya da su zauna lafiya.

“Canada na kira da a dakatar da tashin hankali cikin gaggawa kuma a shirye take ta taimaka wajen cimma hakan,” in ji shi.
Trump da Khamenei.
Shugaba Donald Trump na Amurka da tsohon jagoran addinin Iran, Ayatolla Khamenei Hoto: Win Mcnamee
Source: Twitter

Ya kuma soki rashin tuntubar kungiyoyin kasa da kasa, yana mai cewa Amurka da Isra’ila sun dauki mataki bisa ra'ayin kansu ba tare da tuntubar Majalisar dinkin duniya ba, cewar rahoton Gulf News

Iran ta jawo wa Amurka babbar asara

A wani rahoton, kun ji cewa an kiyasta cewa kasar Amurka ta yi asarar kayan aikin soja da kudinsu ya kai kusan Dala biliyan 1.9 sakamakon hare-haren Iran.

Alkaluman kididdigar da aka tattara sun nuna cewa hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kaddamar sun janyo babbar asara ga kadarorin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Iran ta kai hari kan sansanonin soja da ofisoshin jakadancin Amurka a kasashe da dama na Gabas ta Tsakiya bayan harin da aka kai mata, lamarin da ya jawowa Amurka asara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262