Babbar Magana: Wasu Dakarun Iran Sun Yi Yunkurin Kashe Shugaban Amurka, Trump

Babbar Magana: Wasu Dakarun Iran Sun Yi Yunkurin Kashe Shugaban Amurka, Trump

  • Amurka ta yi ikirarin cewa kasar Iran ta kafa wata runduna ta musamman domin shirya yadda za a kashe shugaban kasa, Donald Trump
  • Ma'aikatar tsaron Amurka ta yi ikirarin cewa dakarun sojojin kasar sun yi nasarar jagoran wannan runduna da ke shirin ganin bayan Trump
  • Ministan tsaro, Pete Hegseth ya tabbatar da faruwar hakan, ya ce an kashe jami'in na Iran ne a jiya Talata, 3 ga watan Maris, 2026

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Gwamnatin Amurka ta yi ikirarin cewa ta gano shirin wasu jami'an Iran na kashe shugaban kasa, Donald J. Trump.

Ta bayyana cewa sojojin Amurka sun kashe babban jami’in Iran da ke jagorantar wata runduna da ake zargin ta shirya yunkurin kashe Shugaba Donald Trump.

Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump a fadar White House, Washington D.C Hoto: Win Mcnamee
Source: Getty Images

Rahoton tashar Al-Jazeera ya tattaro cewa Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ce ta sanar da hakan, a ranar Laraba, 4 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

Amurka ta kashe babban jami'in Iran

Sanarwar kisan jami’in, wanda ba a bayyana sunansa ba, ta fito ne yayin karin bayani kan yakin da Amurka ta fara yi da Iran a hedkwatar Pentagon.

Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yaba da kisan jami'in na Iran, wanda ya ce an kashe shi a ranar Talata yayin da yaki tsakanin kasashen ke kara zafi.

“Mun farauto jagoran rundunar da ta yi yunkurin kashe Shugaba Trump kuma an kashe shi. Iran ta yi kokarin kashe Shugaba Trump, amma shi ne yi nasara a karshe,” in ji Hegseth ga manema labarai.

Yadda aka fara zargin yunkurin kashe Trump

A 2024, Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta gurfanar da wani dan Iran bisa zargin cewa rundunar juyin juya hali ta Iran ta sa shi shirya kisan Trump, wanda a lokacin yake zababben shugaban kasa.

Sai dai gwamnatin Iran ta musanta zargin cewa ta yi niyyar kashe Shugaba Trump ko wasu jami’an Amurka, kamar yadda Reuters ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da yaki, Trump ya yi magana kan kasancewar Iran a gasar cin kofin duniya a Amurka

Trump ya ambaci wannan yunkuri a wata hira da ya yi ranar Lahadi, bayan harin hadin gwiwae Amurka da Isra’ila ya kashe Jagoran Addinin Iran, Ali Khamenei, inda ya ce: “Na same shi kafin ya same ni.

Pete Hegseth.
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth a hedkwatar Pentagon Hoto: Alex Wong
Source: Getty Images

Sai dai Hegseth ya ce Shugaba Trump bai taba bayar da umarnin cewa a bai wa farautar jagoran rundunar da take son kashe shi muhimmanci ba.

“Ko kadan ba shi ne babban abin da muka sa a gaba ba, kuma shugaban kasa ko wani bai taba taso da batun ba amma ni da wasu mun tabbatar cewa wadanda ke da alhakin hakan sun shiga cikin jerin wadanda muka kai wa hari,” in ji shi.

Amurka ta murkushe jirgin ruwan Iran

A dazu, mun kawo rahoton cewa wani jirgin ruwan yaƙi na ƙasar Amurka wanda ke tafiya a ƙarƙashin ruwa ya harba makamin torpedo kan jirgin ruwan yakin Iran.

Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth ya bayyana cewa wannan harin da aka kai wa jirgin ruwan yaƙin na Iran shi ne irin hari na farko da aka kai tun bayan yaƙin duniya na biyu.

Gwamnatin Sri Lanka ta bayyana cewa ta gano gawarwaki da dama sannan ta ceto sojojin ruwa 32 da suka jikkata bayan da jirgin yaƙin na Iran ya nutse.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262