Yadda Dan Khamenei da zai Iya Gadonsa, Mojtaba Ya Tsallake Harin Amurka da Isra'ila
- Dan marigayi Ayatollah Ali Khamenei mai suna Mojtaba ya tsallake hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai Iran a karshen makon da ya wuce
- Wasu majiyoyin gwamnatin Iran sun bayyana dalilan da suka sanya Mojtaba Khamenei tsira daga harin da ya kashe mahaifinsa a birnin Tehran
- Amurka ta hada kai da Isra'ila wajen kai munanan hare-hare Iran yayin da suke tsaka da tattaunawa game batun makamin nukiliya da sauransu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran, Iran - Majiyoyi sun ce Mojtaba Khamenei, wanda ake ganin zai iya zama Jagoran Addini a Iran, ya tsira daga hare-haren da aka kai Tehran.
Mojtaba Khamenei, ɗan marigayi Jagoran Addini na Iran, ya tsira daga hare-haren sama na Amurka da Isra’ila da aka kai wa Iran inda aka kashe mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei.

Kara karanta wannan
Yaki na kara zafi da Amurka, an ji shirin da Iran take yi na nada magajin Ayatollah Khamenei

Source: Getty Images
Mojtaba Khamenei yana raye
Wasu majiyoyi biyu na Iran sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters a ranar Laraba, 4 ga Fabrairun 2026 cewa Mojtaba Khamenei yana na da rai har yanzu.
An nemi karin bayani game da halin da ya ke ciki ne a lokacin da aka yawaita magana kan cewa zai iya maye gurbin mahaifinsa da aka kashe.
Dalilin kubutar Mojtaba daga harin Amurka
Wata majiya mai tushe daga kasar Iran ta jaddada cewa ba abin da ya samu Mojtaba Khamenei kuma yana cikin koshin lafiya a halin yanzu.
“Yana nan da rai ... bai kasance a Tehran ba lokacin da aka kashe Jagoran Addinin,”
- Inji ɗaya daga cikin majiyoyin.
An kashe mahaifinsa ne a ranar Asabar bayan Amurka da Isra’ila sun kai hare-hare kan wurare daban-daban a fadin Iran – cikin jerin manyan jami’an soja da sauran masu tasiri a kasar.

Kara karanta wannan
Yadda kisan Khamenei zai shafi 'yan Shi'a a Najeriya, rashinsa ya 'hada' kan Musulmi
Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran ne suka sanar da mutuwar Khamenei a ranar Lahadi bayan kai harin da safiyar ranar Asabar.
Wane ne Mojtaba Khamenei a Iran?
Tashar Al-Jazeera ta ce ana kallon Mojtaba a matsayin wanda tsarin mulkin ƙasar ke gani a matsayin mai yiyuwar gadon kujerar mahaifinsa.
Mojtaba Khamenei ya kasance malamin addini ne mai matsakaicin matsayi wanda ke da kusanci da rundunar juyin juya halin Iran.
Baya ga kasancewarsa malamin addini, ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu tasiri a tsarin malamai na Iran.
Tun kafin kashe Ayatollah Ali Khamenei, shekaru da dama ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan mutanen da za su iya maye gurbin mahaifinsa.

Source: Twitter
Amurkawa sun makale a kasashe
A wani labarin, kun ji cewa Amurkawa na cigaba da korafi a kasashen Gabas ta Tsakiya yayin da Iran ke cigaba da harba makamai zuwa kasashe daban-daban.
Wasu 'yan Amurka da suka makale a Dubai sun bukaci gwamnatin shugaba Donald Trump ta gaggauta ceto su daga halin fargaba da suke ciki.
Ministan harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa suna kokarin ganin sun kubutar da Amurkawa, inda ya ce sama da mutum 1,500 sun nemi agaji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng