Isra'ila Ta Fadi Sunan Wani Babba da Ta ke Shirin Hallaka wa a Kasar Iran

Isra'ila Ta Fadi Sunan Wani Babba da Ta ke Shirin Hallaka wa a Kasar Iran

  • Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz ya yi barazana ga sabon Ayatollah, wato jagoran addini da Iran ke shirin nada wa bayan hallaka Ali Khamenei
  • Israel Katz ya ce sun yi shiri na musamman domin a kawar da duk sabon shugaban da jamhuriyyar Musulunci ta Iran za ta nada
  • Ya jaddada cewa Isra’ila za ta hada kai da Amurka domin lalata karfin Iran yayin da ake ci gaba da samun musayar wuta a tsakanin kasashen uku

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Tel Aviv, Israel – Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya bayyana cewa kasarsa za ta yi yunkurin kawar da duk wani shugaba da za a nada domin maye gurbin jagoran addini na Iran, Ali Khamenei.

A wata sanarwa da ya fitar, Katz ya ce duk wanda gwamnatin Iran ta nada domin ci gaba da jagorantar kasar zai zama silar kaddamar da sabon hari.

Kara karanta wannan

Baya ta haihu: Amurka ta zare hannu a kashe Khamenei, ta fadi mai laifi

Isra'ila ta fara harin shugaba a Iran
Benjamin Netanyahu, Firaministan Isra'ila Hoto: Getty
Source: Facebook

Aljazeera ta wallafa cewa ya bayyana haka ne a yayin da ya ke ikirarin cewa kasarsa da taimakon Amurka ba za ta saurara wa Iran ba.

Mistan Isra'ila ya yi barazana ga Iran

Daily Post ta wallafa cewa Katz ya bayyana cewa ba za su saurara ba wajen kade abin da ya kira barazana ga Isra'ila, Amurka da sauran kasashen duniya.

Ya ce:

“Duk wani shugaba da gwamnatin Iran ta nada domin ci gaba da jagorantar shirin lalata Isra’ila, barazana ga Amurka da kasashen yankin, tare da danniya ga al’ummar Iran, zai zama makasudi kai hari tsaye don kawar da shi."

Ya kara da cewa ba sunan sabon shugaban ba ne ke da muhimmanci, ko kuma inda zai zauna idan an zabe shi.

A cewarsa, duk wanda ya karbi jagoranci domin ci gaba da manufofin da Isra’ila ke ganin barazana ce, ba zai tsira daga shirin da suke yi ba.

Kara karanta wannan

An ji duriyar Firaministan Isra'ila, Netanyahu ana tsaka da rade radin Iran ta tura shi lahira

Rikicin Iran, Isra'ila da Amurka na kazanta

Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Isra’ila da Iran ke kara tsananta, musamman dangane da batutuwan tsaro da siyasa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Isra'ila ta yi sabon alwashi bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei
Ayatollah Khamenei wanda harin Isra'ila da Amurka Hoto: Getty
Source: Getty Images

Ministan tsaron ya kuma bayyana cewa Isra’ila za ta ci gaba da aiki tare da Amurka domin lalata karfin soji da na fasaha da Iran ke da shi.

Ya ce manufarsu ita ce rage ikon Iran wajen aiwatar da abin da ya kira barazana ga tsaron yankin da kuma duniya baki daya.

A cewarsa, wannan hadin gwiwa da Amurka zai taimaka wajen samar da yanayin da zai ba wa al’ummar Iran damar kifar da gwamnatinsu.

Katz ya zargi gwamnatin Iran da danniya da tauye ‘yancin jama’a, yana mai cewa al’ummar kasar na bukatar sauyi.

Yaki da Iran: Za a fara Al-Kunut

A baya, mun wallafa cewa Shugaban kungiyar Izala, wato JIBWIS, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya umarci limamai su fara gudanar da addu’ar Al-Kunutu a masallatai.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Trump ya fadi wasu dalilai 2 da suka sa ya kai hare hare Iran

Sheikh Bala Lau ya ce mafi yawan wadanda rikice-rikicen ke shafa Musulmi ne da ba su da laifi, yana mai nuna alhini kan salwantar rayuka a yakin da Amurka da Isra'ila suka jawo.

Shugaban kungiyar ta Izala ya roki Allah SWT ya kawo karshen zubar da jini tare da dawo da zaman lafiya a duniya da Najeriya baki daya, tare da samun wanzuwar kwanciyar hankali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng