An Saki Hotunan Sojojin Amurka da Kasar Iran Ta Hallaka da Bama Bamai
- Gwamnatin Amurka ta fitar da hotunan wasu daga cikin sojojinta da suka mutu bayan makamai da Iran ta harba a Gabas ta Tsakiya
- Rahotanni sun nuna cewa sojojin da suka mutu suna bakin aiki ne yayin da makaman Iran suka dura kansu a ranar Lahadi bayan fara yaki
- Shugabanni da wasu mutanen Amurka sun nuna damuwa da mutuwar sojojin, yayin da wasu ke sukar gwamnatin Trump kan shiga yakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - An wallafa hotuna da sunayen hudu daga cikin sojojin Amurka shida da aka kashe a yaƙin Iran a ranar Lahadin da ta wuce.
Pentagon ta bayyana sunayensu a ranar Talata a matsayin mambobin rundunar soji masu jiran ko-ta-kwana daga jihohi daban-daban, waɗanda ke aiki a fannin dabaru da samar wa dakaru abinci da kayan aiki.

Source: Twitter
Yadda aka kashe sojojin Amurka
Rahoton PBS ya nuna cewa sun mutu ne lokacin da wani jirgi mara matuƙi ya kai hari kan cibiyar Shuaiba, Kuwait, kwana guda bayan Amurka da Isra’ila sun kaddamar da yaƙin soji kan Iran.
Iran ta mayar da martani da harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra’ila da wasu ƙasashen Larabawa na yankin Gulf da ke karɓar bakuncin sojojin Amurka.
Sunayen sojojin Amurka da aka kashe
Rahoto ya nuna cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da Kyaftin Cody Khork, mai shekara 35, daga yankin Winter Haven a jihar Florida.
Sajan Noah Tietjens mai shekara 42, daga Bellevue, a jihar Nebraska na cikin sojojin da suka rasu bayan harin da Iran ta kai musu.
Haka zalika Sajan Nicole Amor mai shekara 39, daga White Bear Lake a jihar Minnesota ta kwanta dama bayan harin da ka kai musu.

Source: Twitter
Na hudu cikin wadanda aka fitar da sunansu shi ne Sajan Declan Coady, mai shekara 20, daga West Des Moines a jihar Iowa, wanda aka karawa matsayi bayan rasuwarsa.
Abin da Amurkawa ke fada kan sojojin
Shafin 'yan majalisun jam'iyyar Republican ya wallafa sakon ta'aziyya a X, inda ya ce dakarun sun sadaukar da rayuwarsu wajen kare Amurka:
"Muna godiya ga jaruman Amurka da suka kare mu daga barazanar tsattsauran ra’ayin Iran.
Kun bayar da cikakkiyar sadaukarwa, kuma ba za a taɓa mantawa da hidimarku ga ƙasarmu ba."

Source: Twitter
Gwamnan Minnesota, Tim Walz ya wallafa a X cewa yana cikin jimamin rasuwar Sajan Nicole M. Amor 'yar yankin White Bear Lake da aka kashe a Kuwait.
Ya ce:
"Ya bayar da ranta wajen yi wa jiharmu da ƙasarmu hidima."
Sojojin Amurka sun kai hari Ecuador
A wani labarin, kun ji cewa sojojin Amurka sun sanar da cewa sun kaddamar da manyan hare-haren hadin gwiwa a kasar Ecuador.
Gwamnatin kasar Ecuador ta tabbatar da kai hari, duk da cewa ta ce ba za ta yi karin bayani game da abubuwan da suka faru ba.
'Yan kwanaki kafin kai farmakin, shugaban kasar Ecuador ya gana da kwamandan sojojin Amurka da ke lura da yankin da aka kai farmakin.
Asali: Legit.ng

