Ba a Gama da Iran ba, Amurka Ta Kaddamar da Hare Hare a Kasar Ecuador

Ba a Gama da Iran ba, Amurka Ta Kaddamar da Hare Hare a Kasar Ecuador

  • Rundunar sojin Amurka sun kaddamar da sababbin hare-hare a wani yanki na kasar Ecuador kamar yadda ta sanar a ranar Talata, 3 ga Fabrairun 2026
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da gwabza yaki da Iran da Amurka/Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya bayan kashe Ayotollah Ali Khamenei
  • Gwamnatin kasar Ecuador ta yi magana bayan harin kamar yadda kwanmandan sojojin Amurka ya yi karin haske ga manema labarai a wata sanarwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ecuador - Sojojin Amurka da na Ecuador sun fara kai farmakin hadin gwiwa domin yaki da safarar miyagun kwayoyi a wasu yankuna.

Rundunar sojin Amurka ta bayyana cewa ta kai wani farmaki a ranar Talata a Ecuador, sai dai bangarorin biyu ba su bayar da karin bayani ba.

Kara karanta wannan

Makaman Iran sun dura kan tankar man Amurka a teku, ta kama da wuta

Shugaban Amurka Donald Trump
Jirgin Amurka a hagu, Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amurka ta kai hari kasar Ecuador

The Guardian ta rahoto cewa rundunar Amurka da ke kula da kasashe 31 a yankin Caribbean da sauransu ta sanar da kai hari wani yanki na Ecuardor.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin X, rundunar sojin Amurka ta bayyana harin a matsayin “mataki mai karfi” da ke da nufin yaki da safarar miyagun kwayoyi ba bisa ka’ida ba.

Amurka ta ce ta kai harin ne tare da hadin gwiwar Ecuador:

“Muna ɗaukar mataki mai ƙarfi tare domin fuskantar ‘yan ta’adda, waɗanda suka daɗe suna haddasa tsoro, tashin hankali da rashawa ga al’ummar yankin nahiyar nan."

Kwamandan rundunar, Janar Francis L. Donovan ya kara da cewa:

“Mun yaba wa maza da mata na rundunar sojin Ecuador bisa jajircewarsu a wannan fafutuka, inda suke nuna jaruntaka ta hanyar ci gaba da ɗaukar matakai kan ‘yan ta’adda a ƙasarsu.”

Bayanin kasar Ecuador kan harin

Kara karanta wannan

Iran ta ce ta kashe sojojin Amurka 500 a luguden wuta da ta masu

Bayan kai farmakin, ma’aikatar tsaron kasar Ecuador ta ce ba za ta yi cikakken bayani kan hare-haren da ake kaiwa kan 'yan ta'addan ba.

Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan kasar da ke Kudancin Amurka ta ce Washington ya shiga wani “sabon mataki” a abin da ta kira yaki da miyagun kwayoyi.

Shugaban Ecuador, Daniel Noboa, wanda ake ganin na kusa da Donald Trump ne, ya ce Washington na daga cikin kawayen yankin da ke shiga aikin yaki da kungiyoyin safarar miyagun kwayoyi.

Shugaban kasar Ecuardor
Shugaban Ecuardor, Daniel Noboa a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A ranar Litinin, Noboa ya gana da shugaban rundunar, Francis Donovan da kuma shugaban rundunar ayyuka na musamman a yankin, Mark Schafer.

A yayin ganawar, sun tattauna shirye-shiryen musayar bayanai da daidaita ayyuka a filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa, kamar yadda ofishin Noboa ya bayyana a wata sanarwa.

Ga bidiyon da dakarun na Amurka ta fitar kan harin:

Amurka na sabon shiri kan Iran

A wani labarin, kun ji cewa, ana zargin Shugaban Amurka, Donald Trump ya fara sabon shiri domin tunkarar kasar Iran ta bayan fage.

Kara karanta wannan

Sanatocin Amurka sun kada kuri'a kan hana Trump cigaba da yaki da Iran

Wasu rahotanni sun ce Trump na tattaunawa da shugabannin Kurdawa da ke dauke da makamai a Iran kan yadda za su hargitsa kasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake gwabza yaki tsakain Amurka da Iran bayan wani hari da Trump ya kai tare da goyon bayan Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng