Trump Ya Fadi Adadin Shugabannin Iran da Aka Kashe, Ya Bayyana Mamakin da Kasar Ta Ba Shi
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan yakin da kasarsa ke gwabzawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Donald Trump ya bayyana cewa Amurka ta samu nasarar kashe shugabannin Iran da dama bayan sun taru a wuri guda
- Shugaban na Amurka ya bayyana cewa akwai hare-hare masu zafi da dakarunsa za su kai kan Iran nan gaba kadan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Amurka - Shugaban ƙasar Amurka ya yi magana kan fadan da ake gwabzawa tsakanin kasarsa da Iran.
Mista Donald Trump ya bayyana cewa "babban hari" na soja da Amurka za ta ɗauka kan kasar Iran yana nan tafe.

Source: Facebook
Donald Trump ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar CNN a ranar Litinin, 2 ga watan Maris 2026.
Donald Trump ya ce manyan hare-hare na gaba

Kara karanta wannan
Bayan kashe 'dan kasarta, China ta maida martani kan yakin Iran da Amurka, Isra'ila
Shugaban kasar na Amurka ya bayyana hare-haren da ake kaiwa yanzu a matsayin farkon wani gagarumin farmaki.
“Ba mu ma fara ba su kashi sosai ba. Babban harin bai riga ya auku ba. Babban na nan tafe nan ba da jimawa ba."
- Donald Trump
Game da tsawon lokacin da rikicin zai ɗauka, Trump ya ce:
“Ba na son ganin abin ya yi tsayi da yawa. Kullum ina tunanin zai ɗauki makonni huɗu ne. Kuma a halin yanzu ma mun ɗan wuce lokacin da muka tsara.”
Wane mamaki kasar Iran ta ba Trump?
Shugaban ya kuma bayyana cewa “babban abin mamaki” shi ne hare-haren da Iran ta kai wa ƙasashen Bahrain, Jordan, Kuwait, Qatar, da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Haka kuma, ya yi ikirarin cewa an kashe shugabannin Iran guda 49 a hare-haren farko da aka kai.
Trump ya ce Iran ta rasa “shugabanni da dama” sakamakon hare-haren farko da aka kai musu.
“Mutum 49. Wani gagarumin hari ne aka kai. Sun ɗan nuna girman kai ta hanyar yin taro duka a wuri guda."
“Sun ɗauka ba za a iya gano inda suke ba. Ashe za a iya gano su. Mu kanmu mun yi mamakin ganin hakan.”
- Donald Trump

Source: Facebook
Trump ya fadi shirinsa kan Iran
Lokacin da aka tambaye shi ko Amurka tana yin wani abu bayan harin soja domin taimaka wa al’ummar Iran su ƙwato ikon ƙasarsu daga hannun gwamnatin ƙasar, Trump ya ce, “Eh.”
“Lallai muna yin hakan. Amma a yanzu muna son kowa ya zauna a cikin gida. Waje ba shi da aminci a yanzu. Kuma lamarin na gab da ƙara yin muni."
“Ba mu ma fara kai musu hare-hare masu zafi ba. Babban harin bai riga ya faru ba. Babban na nan tafe nan kusa.”
- Donald Trump
Martanin China kan yakin Amurka da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa kasar China ta tsoma baki kan yakin da ake yi tsakanin kasashen Amurka da Iran.
China ta yi kira da a tsagaita wuta, a koma kan teburin tattaunawa domin kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya yayin da ake ci gaba da fafatawa.
Hakazalika, kasar ta bukaci a warware matsalar da jawo yakin tsakanin kasashen uku ta hanyar tattaunawa da sulhu.
Asali: Legit.ng
