Rana Ta 3: Yakin Iran Ya Dauki Wani Salo, Birtaniya Ta ba da Gudunmuwa

Rana Ta 3: Yakin Iran Ya Dauki Wani Salo, Birtaniya Ta ba da Gudunmuwa

  • Salon yaki na shirin sauyawa a Gabas ta Tsakiya yayin da aka shiga rana ta uku a gwabzawar da ake tsakanin Iran da kasashen Amurka da Isra'ila
  • Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ba Amurka damar amfani da sansanin sojinsu wajen kare kai daga hare-haren Iran a wata sanarwa da ya fitar
  • A kwanakin baya, shugaban Amurka, Donald Trump ya nemi a ba shi damar amfani da sansanin amma Birtaniya ta ce hakan ba zai yiwu ba sam

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Britain - Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya ce Amurka za ta iya amfani da sansanonin sojinsu domin kai hare-haren kariya kan Iran

Keir Starmer ya bayyana cewa sun amince da bukatar Amurka na amfani da sansanonin sojin Birtaniya domin kai hare-haren kariya kan makaman Iran.

Kara karanta wannan

Yadda Saudiyya ta kakkabo wasu makamai da Iran ta harba a yaki da Amurka

Keir Starmer da Shugaba Donald Trump
Keir Starmer da Donald Trump a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Birtaniya ta taya Amurka yakar Iran

Rahoton Reuters ya nuna cewa Keir Starmer ya ba Amurka damar amfani da sansanin ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Maris, 2026.

Keir Starmer ya ce:

“Amurka ta nemi izinin amfani da sansanonin Birtaniya domin aikin kariya mai iyaka. Mun yanke shawarar amincewa da wannan bukata domin hana Iran harba makamai masu linzami a fadin yankin,”

Starmer ya sake jaddada cewa Birtaniya ba ta shiga cikin hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila da aka kai kan Iran ba, wadanda suka kashe Jagoran Addini na kasar, Ali Khamenei.

Bugu da kari, ya bayyana cewa Birtaniya ba za ta shiga hadin gwiwar kai karin hare-hare ba ga Iran, shigarsu yakin zai tsaya ne ga bayar da damar amfani da sansani kawai.

An kai hari kusa da 'yan Birtaniya

Starmer ya ce Iran ta mayar da martani ta hanyar kaddamar da hare-hare a fadin yankin, inda makaman ta suka kai hari kan filayen jiragen sama da otel-otel da ‘yan Birtaniya ke sauka.

Kara karanta wannan

Yawan sojojin Amurka da suka mutu bayan harin Iran, wasu da dama sun jikkata

“Shawarar da muka yanke ita ce cewa Birtaniya ba za ta shiga kai hare-hare kan Iran ba, musamman ganin cewa muna da yakinin cewa mafita mafi dacewa ga yankin da duniya baki daya ita ce ta hanyar sasanci, inda Iran za ta amince da watsi da duk wani buri na kera makamin nukiliya,”
“Amma duk da haka Iran na kai hare-hare kan kadarorin Birtaniya, tana kuma jefa ‘yan kasarta cikin babban hadari.”

Ya kara da cewa mutanen Birtaniya a yankin Gulf sun bukaci ta kara daukar matakai wajen kare su, kuma wajibi ne a kansa ya kare rayukan ‘yan Birtaniya.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Donald Trump yana yi wa Amurkawa bayani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce jiragen yakin Birtaniya sun riga sun shiga cikin ayyukan kariya na hadin gwiwa, inda suka tare wasu hare-haren Iran, amma hanya daya tilo ta kawar da barazanar ita ce lalata makaman tun daga tushensu a ma’ajiyar ajiya ko wuraren harba su.

Al-Jazeera ta wallafa bidiyon da Stermer a kafar X:

Matsayar Najeriya kan yakin Iran

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi gargadi game da yakin da ke cigaba da gudana a Gabas ta Tsakiya.

Mukaddashin sufeton 'yan sanda, Olatunji Disu ya bukaci kwamishinoni su saka ido a yankunan Najeriya, musamman Arewacin kasar.

Kakakin 'yan sanda na kasa ya bayyana cewa ba za su bar Najeriya ta zama fagen yaki tsakanin kasashen duniya ba, za su tabbatar da tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng