Da Gaske Harin Iran Ya Hallaka Benjamin Netanyahu? An Samu Gaskiyar Lamarin
- Wani sakon a shafukan sadarwa ya yi ikirarin cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya mutu a harin jirgi mara matuki
- Binciken gaskiya ya tabbatar da cewa Netanyahu na raye kuma yana ci gaba da rike mukaminsa na Firaminista
- Kotun ICC ta nuna akwai sammacin kama shi tun 21 Nuwamba 2024, alamar yana fuskantar shari’a amma bai mutu ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Wani sako da ya yadu a kafofin sadarwa ya bayyana cewa Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya mutu.
Hakan na zuwa bayan kasar Iran ta tabbatar da kisan jagoran Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei sakamakon harin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila.

Source: Getty Images
Rahoron da shafin Media Trend Reserver ya wallafa a X ya ce wai harin jirgi marar matuki ya hallaka Benjamin Netanyhau a gidansa da ke Tel Aviv a Isra'ila.
Sakon da aka wallafa a ranar 28 ga Fabrairun 2026, mutane samu kusan kallon mutane 954,000 su ka gani da kuma yada wa sama da 1,100 da kuma mutane 7,700 da suka goyi baya cikin kankanin lokaci.
Meye gaskiyar labarin kisan Netanyahu?
Sai dai binciken gaskiya da Legit.ng ta gudanar ya tabbatar da cewa ikirarin ba gaskiya ba ne.
Majiyoyi masu inganci da dama sun tabbatar da cewa Netanyahu na raye kuma yana ci gaba da zama Firaministan Isra’ila.
Bayanan da ke shafin yanar gizon gwamnatin Isra’ila sun nuna ranar haihuwarsa da mukaminsa na yanzu, ba tare da wata sanarwar rasuwa ba.
Haka zalika, shafin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya watau ICC ya nuna cewa an bayar da sammacin kama shi a ranar 21 ga Nuwamba, 2024, lamarin da ke nuna yana raye kuma yana fuskantar shari’a.
Don haka, rahoton da ya yadu a kafafen sada zumunta ya kasance na karya kuma mai yaudarar jama’a.

Source: Twitter
Wanene Benjamin Netanyahu?
A cewar gwamnatin Isra’ila, an haifi Benjamin Netanyahu a 1949 a Tel Aviv, ya taso a birnin Kudus (Jerusalem).
Ya yi karatun sakandare a Amurka, inda mahaifinsa, Benzion Netanyahu, ya koyar da tarihi, daga baya ya koma Isra’ila a 1967 inda ya shiga rundunar sojin kasar (IDF).
Ya yi aiki a rundunar Sayeret Matkal, wata runduna ta musamman, kuma ya halarci ayyuka da dama ciki har da ceton fasinjojin jirgin Sabena da aka sace a 1972.
Bayan ya yi ritaya daga soja, ya halarci yakin Yom Kippur na 1973, inda aka daga masa mukami zuwa kaftin a rundunar ajiyar soja, cewar Britannica.
Netanyahu ya samu digirin farko a fannin gine-gine da kuma digirin digirgir a harkar kasuwanci daga MIT, sannan ya kuma karanci siyasa a MIT da jami’ar Harvard.
Isra'ila da Amurka sun hallaka Khamenei
Tun farko, an ji cewa kasar Iran ta tabbatar da kisan jagoran Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei sakamakon harin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila.
An kashe jagoran ne a ofishinsa dake rukunin Beit Rahbari yayin da yake gudanar da ayyukansa na yau da kullum a ranar Asabar 28 ga watan Fabrairun 2026.
Iran za ta gudanar da zaman makokin kwanaki 40 yayin da Isra'ila ta kaddamar da sababbin hare-hare kan makaman linzamin kasar.
Asali: Legit.ng

