Iran Ta Dauki Manyan Matakai 3 bayan Amurka Ta Kashe Jagoran Musulunci, Khamenei
Iran - Bayan tabbatar da mutuwar Ayatollah Ali Khamenei, sakamakon hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra'ila a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, gwamnatin Iran ta dauki wasu tsauraran matakai.
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Imam Ayotallah Khamenei, wanda ya rasu yana ɗan shekara 86, ya kasance jagoran ƙasar tun shekarar 1989.

Source: Twitter
An tabbatar da mutuwar Khamenei
Kafar wata labarai ta NBC News ta rahoto kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran yana cewa:
"Ana sanar da al'ummar Iran cewa, Ayatollah Khamenei, jagoran addinin Musulunci, ya yi shahada a wani harin haɗin gwiwa da la'ananniyar ƙasar Amurka da kuma haramtacciyar ƙasar Isra'ila suka kai."
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"Wannan babban malami kuma gwarzon mayaƙi ya sadaukar da rayuwarsa domin ɗaukakar Iran da Musulunci, kuma insha Allahu, yana tare da Imam (Khomeini) da Shugaban Shahidai (Imam Hussain)".
Shafin Telegram na gidan talabijin na ƙasar, IRIB, shi ma ya tabbatar da wannan labari, inda ya ce:
"Jagoran al'umma, jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Mai Girma Ayatollah Khamenei, ya yi shahada."
Manyan matakai 3 da Iran ta dauka
Ga matakai guda uku da Iran ta dauka bayan kisan Khamenei:
1. Zaman makoki da hutun jama'a
Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran sun sanar da dokar yin zaman makoki na kwanaki 40 a faɗin ƙasar domin girmama Khamenei.
Wannan mataki ya haɗa da bayar da hutun kwanaki bakwai a jere, inda aka rufe dukkan ofisoshin gwamnati, makarantu, da wuraren kasuwanci, in ji rahoton The Business Standard.
Gidan talabijin na ƙasar ya nuna sanarwar tare da bayyana mutuwarsa a matsayin "shahada," inda aka yi kira ga jama'a da su kiyaye wannan lokaci.
2. Tsarin miƙa ragamar shugabanci
Dangane da tanadin kundin tsarin mulkin Iran, an kafa wata majalisar shugabanci domin jan ragamar ƙasar a wannan lokaci da ake shirin sauya shugaba.
Wannan hukuma mai mambobi uku ta haɗa da:
- Shugaba Masoud Pezeshkian.
- Shugaban sashin shari'a na ƙasa.
- Wani babban malami daga majalisar Guardian Council.
An ɗora wa wannan majalisa nauyin tabbatar da zaman lafiya da lura da harkokin yau da kullum har sai majalisar kwararru ta zaɓi sabon babban jagora, in ji rahoton Aljazeera.
An riga an fara tsarin zaɓen magajin Khamenei, kodayake ba a bayyana takamaiman lokacin da za a kammala ba saboda matsalolin tsaro.

Source: Twitter
3. Matakan tsaro da harin ramuwar gayya
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun fito fili sun ɗora wa Amurka da Isra'ila alhakin harin, inda suka yi rantsuwar daukar fansa ta hanyar kai hare-hare masu tsanani.
Tuni dai Iran ta ƙaddamar da hare-haren makami mai linzami kan wasu wurare a Isra'ila da ƙasashen Gulf jim kaɗan bayan tabbatar da mutuwar Khamenei, in ji rahoton KGNS News.
A cikin gida kuma, hukumomi sun tsaurara tsaro, inda aka tura dakarun IRGC domin murƙushe zanga-zanga da kiyaye doka a daidai lokacin da ake samun hatsaniya da kuma bukukuwan murna a wasu yankuna.
An kuma yanke intanet a faɗin ƙasar domin taƙaita sadarwa tsakanin masu adawa da gwamnati.
An kashe Ayotallah Khamenei a Iran
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Iran ta tabbatar da kisan jagoran Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei sakamakon harin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila.
An kashe jagoran ne a ofishinsa dake rukunin Beit Rahbari yayin da yake gudanar da ayyukansa na yau da kullum a ranar Asabar.
Iran za ta gudanar da zaman makokin kwanaki 40 yayin da Isra'ila ta kaddamar da sababbin hare-hare kan makaman linzamin kasar.
Asali: Legit.ng


