Rundunar Iran ta IRGC Ta Lashi Takobin Ɗaukar Fansa kan Kisan Khamenei
- Iran ta tabbatar da mutuwar jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren Amurka da Isra’ila da aka kai masu
- Gwamnatin Iran ta ayyana kwanaki 40 na zaman makoki da hutun jama’a bakwai domin jimamin wannan babban rashi da ya same su
- Rundunar tsaron ƙasar ta IRGC ta yi alkawarin ɗaukar fansa kan waɗanda ta kira “makasan” jagoran addini a Iran
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Iran – Kafafen yaɗa labaran gwamnati a Iran sun sanar da cewa jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, ya rasu sakamakon hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai.
Rahoton ya ce an kashe jagoran mai shekaru 86 tare da wasu daga cikin ‘yan uwansa da ke tare da shi a lokacin a hare-haren.

Source: Twitter
TRT ta wallafa cewa tashar talabijin ta gwamnati ta bayyana cewa an ayyana kwanaki 40 na zaman makoki a faɗin ƙasar.
Iran ta ba da hutu bayan kisan Khamenei
Kasar Iran ba bayar da hutun na kwanaki bakwai domin al’ummar kasar su yi alhinida makoki kashe jagoransu, Ayatollah Khamenei.
Khamenei ya shafe sama da shekaru talatin yana jagorantar Iran, tun bayan hawansa mulki a shekarar 1989, inda ya sha jan daga da Amurka da Iran.
Rahotanni sun kuma ce ‘yarsa, surukinsa da jikarsa suna cikin waɗanda suka rasa rayukansu a hare-haren da aka kai a lokacin suna tare da shi.
Rundunar IRGC ta lashi takobin daukar fansa
A martaninta, rundunar IRGC ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta yi alkawarin hukunta waɗanda ta zarga da hannu a kisan jagoran.
Rundunar ta bayyana lamarin a matsayin babban abin takaici da kuma laifi mai girma wanda ba za bari na
Sanarwar ta ce:
"Hannun ramuwar gayya na al’ummar Iran ba zai kyale wadanda suka kashe jagoran al’umma ba. Za a ɗauki mataki mai tsauri, mai ƙarfi kuma mai radadi a kansu.”

Source: UGC
Wannan lamari ya ƙara ɗaga hankulan jama’a a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake fargabar cewa rikicin zai iya ƙara tsananta.
Masu sharhi na siyasa na ganin cewa matakin da Iran za ta ɗauka a nan gaba zai iya shafar tsaron yankin da ma dangantakar ƙasashen duniya baki ɗaya.
Sanarwar Iran ta jaddada cewa ƙasar za ta ci gaba da bin tafarkin jagoranta duk da wannan babban rashi, babu abin da za a fasa.
Ana alhinin rasuwar Khamenei
Ammar Wakili Shanono, matashi ne a Kano Ya shaida wa majiyar Legit cewa kisan babban jagoran ya girgiza kowa.
Ya ce:Mutuwa a tafarkin addini abin alfahari ne ga ’yan Iran
An bayyana cewa mutuwa a hanya ta kare addini abu ne mai kyau a rayuwar ’yan Iran. A cewar bayanin, mutuwar Ali Khamenei ta zama wata kwarin gwiwa ga ’yan Iran.
"Mutuwa a hanya ta kare addini abune mai kyau a rayuwar yan Iran. Saboda haka mutuwar Khameini kwarin gwiwa ce ga yan Iran."
Jagoran Iran, Ayatollah Khamenei ya rasu
A baya, mun wallafa cewa kasar Iran ta tabbatar da kisan jagoran Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei sakamakon harin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila.
An kashe jagoran ne a ofishinsa dake rukunin Beit Rahbari yayin da yake gudanar da ayyukansa na yau da kullum a ranar Asabar 28 ga watan Fabrairu, 2026.
Iran za ta gudanar da zaman makokin kwanaki 40 yayin da Isra'ila ta kaddamar da sababbin hare-hare kan makaman linzamin kasar bayan kashe jagoran.
Asali: Legit.ng


