Tashin Hankali: Amurka da Isra'ila Sun Kashe Jagoran Addinin Musulunci na Iran
- Kasar Iran ta tabbatar da kisan jagoran Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei sakamakon harin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila
- An kashe jagoran ne a ofishinsa dake rukunin Beit Rahbari yayin da yake gudanar da ayyukansa na yau da kullum a ranar Asabar
- Iran za ta gudanar da zaman makokin kwanaki 40 yayin da Isra'ila ta kaddamar da sababbin hare-hare kan makaman linzamin kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iran - Kafafen yada labaran gwamnatin Iran sun tabbatar da cewa jagoran addinin Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei, "ya yi shahada."
Rahotanni sun tabbatar da cewa, Ayotallah Khamenei ya rasu ne sakamakon harin hadin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai Iran.

Source: Twitter
An kashe jagoran Musulunci na Iran
Kafar wata labarai ta NBC News ta rahoto kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran yana cewa:
"Ana sanar da al'ummar Iran cewa, Ayatollah Khamenei, jagoran addinin Musulunci, ya yi shahada a wani harin haɗin gwiwa da la'ananniyar ƙasar Amurka da kuma haramtacciyar ƙasar Isra'ila suka kai."
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"Wannan babban malami kuma gwarzon mayaƙi ya sadaukar da rayuwarsa domin ɗaukakar Iran da Musulunci, kuma insha Allahu, yana tare da Imam (Khomeini) da Shugaban Shahidai (Imam Hussain)".
Shafin Telegram na gidan talabijin na ƙasar, IRIB, shi ma ya tabbatar da wannan labari, inda ya ce:
"Jagoran al'umma, jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Mai Girma Ayatollah Khamenei, ya yi shahada."
Shugaban Amurka Donald Trump ya riga ya sanar da wannan mutuwa tun da fari, inda ya bayyana cewa hakan ya ba wa ƴan Iran "babbar dama" ta "ƙwato" ƙasarsu.
An ayyana zaman makoki a Iran
Ƙasar Iran za ta gudanar da zaman makoki na kwanaki 40 da kuma hutun kwanaki bakwai domin girmama Khamenei, a cewar rahoton Reuters.
Wannan zaman makoki da hutun za su biyo bayan sanarwar shahadar Ayatollah da gwamnati ta fitar a hukumance, kamar yadda kafar yaɗa labaran Nour News ta sanar a Telegram.

Kara karanta wannan
Iran ta maida martani kai tsaye ga Amurka kan yunkurin kifar da gwamnatin Musulunci

Source: Twitter
An kashe Khamenei ne a ofishinsa
An kashe Khamenei ne yayin da yake cikin ofishinsa, in ji kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran.
"Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya yi shahada ne a wurin aikinsa da ke rukunin Beit Rahbari," in ji shafin Telegram na IRIB.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
"Yana gudanar da ayyukansa na yau da kullum kuma yana ofishinsa a lokacin da ya yi shahada, kuma wannan hari ya afku ne a sa'o'in farko na safiyar ranar Asabar".
Iran ta farmaki sansanonin Amurka
A wani labari, mun ruwaito cewa, Iran ta kai hare-haren makami mai linzami kan sansanonin sojojin Amurka dake kasashen Qatar, Kuwait, Bahrain da UAE.
Akalla mayaka biyu ne suka rasa rayukansu a kasar Iraki sakamakon hare-haren sama da aka kai kan sansanin dakarun Hashid Shaabi.
Hukumomin Bahrain da Qatar sun kunna kararrawar gargadi yayin da suke kokarin kakkabo makaman linzamin da kasar Iran ta harba.
Asali: Legit.ng
