An Rufe Sararin Samaniyar Kasashe 8 da Yaki Ya Barke tsakanin Iran da Amurka
- Akalla kasashe takwas ne suka rufe sararin samaniyarsu sakamakon hare-haren da ake yi tsakanin Amurka da kasar Iran
- Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa Amurka da Isra'ila sun farmaki Iran don lalata wuraren kera makaman nukiliya
- Yayin da ita ma Iran ta mayar da martani, manyan kamfanonin jiragen sama sun soke zirga-zirga ta yankin Gabas ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jerin hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, da kuma martanin da Tehran ta mayar, ya haddasa barkewar tashe-tashen hankula a yankin.
Wadannan hare-hare daga bangarorin biyu ya tilasta rufe sararin samaniyar mafi yawan kasashen Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
An rufe sararin samaniyar kasashe 8
Akalla kasashe takwas ne suka sanar da rufe sararin samaniyar su a ranar Asabar, ciki har da Iran, Isra'ila, Iraki, Jordan, Qatar, Bahrain, Kuwait, da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), in ji rahoton Reuters.

Kara karanta wannan
Amurka da Isra'ila sun kashe jagoran addinin Musulunci na Iran? Gaskiya ta bayyana
Haka kuma, kasar Siriya ta sanar da rufe wani bangare na sararin samaniyarta a kudancin kasar da ke iyaka da Isra’ila na tsawon sa’o’i 12.
Wannan hargitsi ya biyo bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai a fadin Iran, wadanda Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin cewa za su ruguza masana'antar makami mai linzami ta Iran da kuma lalata dakarun ruwanta yanzu.
Iran, wadda take tsaka da tattaunawa da Amurka kan shirinta na nukiliya kafin harin, ta yi rantsuwar mayar da martani mai tsanani.
Hare-haren Iran, Amurka da Isra'ila
Ba tare da bata lokaci ba, Iran ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya a Isra'ila da kuma kasashen Larabawa da ke da sansanonin sojin Amurka.
Wani babban jami'in Iran ya bayyana cewa:
"Daga yanzu dukkan kadarorin Amurka da na Isra'ila da ke a Gabas ta Tsakiya ne abin harinmu. Babu sauran wani shamaki bayan wannan zalunci na yau."
Wannan tashin hankali ya sa kamfanonin jiragen sama na duniya soke ko karkatar da zirga-zirgar jiragensu daga yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya zama muhimmiyar hanya tsakanin Turai da Asiya.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki a rigimar Iran da Isra'ila, Najeriya ta ba da shawara
Rahoton Aljazeera ya nuna cewa kamfanonin jirage irin su Lufthansa, Air France, British Airways, Qatar Airways, da Air India duk sun sanar da dakatar da zirga-zirga yau.

Source: Getty Images
Rikicin Iran, Amurka, Isra'ila zai shafi duniya
Ma’aikatar sufurin kasar Rasha ta ce kamfanoninsu sun dakatar da tashi zuwa Iran da Isra’ila, yayin da Air India ta ce za ta guji daukacin yankin Gabas ta Tsakiya baki daya.
Rahoto ya nuna cewa wannan rikici ya kirkiro wasu tashe-tashen hankula guda biyu masu tafiya tare, wadanda za su iya sa rikicin ya zama mai sarkakiya da yankin bai taba gani ba.
Wannan yanayi ya jefa tattalin arzikin sufurin jiragen sama na duniya cikin wani babban kalubale, musamman ganin cewa sararin samaniyar Rasha da Ukraine ma a rufe yake.
Halin da dan Najeriya yake ciki a Kuwait
A zantawar Legit Hausa da wani matashi Sadiq Madabo, wanda yanzu haka yake zaune a Kuwait, ya shaida cewa babu wata sanarwar gargadi da suka samu cewa za a kai hare-hare.
"Babu wata sanarwa da muka samu cewa wannan yaki zai barke tsakanin kasashe guda biyu, amma dama mun san ana zaman doya da manja tsakanin Isara'ila da Iran da kuma Amurka da ke tare da Isra'ila.

Kara karanta wannan
Rasha ta soki Amurka da Isra'ila bayan sun kai farmaki Iran, ta fadi taimakon da za ta kawo
"Ba mu san da cewa yakin zai sake barkewa ba. Musamman ma mu da muke nan (Kuwait) ba mu san yakin zai zo ya shafi kasashen da muke ciki ba, amma mun san Amurka na da sansanoni a nan (Kuwait) da sauran kasashen Larabawa da ke kewaye da Iran."
- Sadiq Madabo.
Sadiq Madabo ya ce wannan yakin ya zo da sabon salo, domin kuwa shirin da Iran ta yi wannan karon ya fi wanda ta yi a shekarar baya, don haka ba kanwar lasa ba ce.
"A yanzu na ga hakikanin karfin Iran, domin kan ka ce me, sun kai hare-hare a kasashe bakwai na Larabawa. Amma ina rokon Allah ya takaita, don idan ya wuce haka, to wasu kasashe za su iya shiga."
- Sadiq Madabo.
Iran ta farmaki sansanonin Amurka
Kun dai ji cewa, Iran ta kaddamar da hare-haren makami mai linzami kan sansanonin sojojin Amurka dake kasashen Qatar, Kuwait, Bahrain da UAE.
Akalla mayaka biyu ne suka rasa rayukansu a kasar Iraki sakamakon hare-haren sama da aka kai kan sansanin dakarun Hashid Shaabi.
Hukumomin Bahrain da Qatar sun kunna kararrawar gargadi yayin da suke kokarin kakkabo makaman linzamin da kasar Iran ta harba.
Asali: Legit.ng