Iran Ta Sha Alwashi Mai Zafi bayan Israila da Amurka Sun Kai Mata Hari, Ta Fadi Shirinta
- Isra'ila da Amurka sun kaddamar da hare-hare ta sama kan Iran da nufin dakile shirin Tehran na nukiliya da makamai masu linzami
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an ji kararrakin fashe-fashe a wasu biranen Iran biyo bayan hare-haren da aka kawo
- Sai dai, Iran ta nuna ba za ta zuba ido ta bari hare-haren su tafi haka nan kawai ba, inda ta sha alwashin mayar da martani mai zafi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Iran - Kasar Iran ta yi martani kan hare-hare ta sama da kasashen Amurka da Isra'ila suka kai mata.
Iran ta lashi takobin mayar da martani ga hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai mata, inda ta yi alkawarin cewa ramuwar gayyar za ta kasance mai girma.

Source: Twitter
Wani jami’in Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa kasar na shirin kaddamar da hare-haren ramuwar gayya wadanda aka tsara za su kasance masu zafi.
Amurka da Isra'ila sun kai hari Iran
A ranar Asabar ne aka ji kararrakin fashe-fashe a biranen Iran da suka hada da Kermanshah, Lorestan, Tabriz, Isfahan, da kuma Karaj.
Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya bayyana cewa:
"Isra'ila ta kaddamar da hari na rigakafi ne a kan Iran domin kawar da barazanar da ke fuskantar kasar Isra'ila.”
Wannan hari ya biyo bayan wani yakin sama na tsawon kwanaki 12 da aka fafata tsakanin Isra'ila da Iran a watan Yunin 2025.
Haka kuma ya biyo bayan jerin gargaɗi daga Amurka da Isra'ila cewa za su sake kai hari idan Iran ba ta dakatar da shirye-shiryenta na nukiliya da makamai masu linzami ba.
An boye Ali Khamenei
Rahotanni sun nuna cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ba ya birnin Tehran a lokacin da makaman linzamin Amurka da Isra’ila suka afka wa Iran.
An ce an mayar da Ayatollah Ali Khamenei zuwa wani boyayyen wuri mai tsaro.

Source: Getty Images
Iran ta sha alwashin mayar da martani
Sai dai yayin da yake martani kan harin, Ebrahim Azizi, shugaban kwamitin tsaro na majalisar dokokin Iran, ya ce Isra’ila da Amurka sun bi hanyar da ba su da ikon sarrafa karshenta.
Ebrahim Azizi ya yi martanin ne a wani rubutu a shafinsa na X.
“Mun gargaɗe ku! Yanzu kun fara bin hanyar da karshenta ba ya karkashin ikonku."
- Ebrahim Azizi
A nasa bangaren, Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce an kai harin ne domin kare muradun Amurka.
Amurka ta kakkabo jirginta
A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin kasar Amurka sun tafka kuskure yayin da suka kakkabo wani jirgi mara matuki a sararin samaniya.
Sojojin na Amurka sun kakkabo wani jirgi marar matuƙi na hukumar fasa-kwauri da kiyaye iyakoki ta CBP ta hanyar amfani da na'urar laser.
Kuskuren da sojojin suka yi ya tilasta wa hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama (FAA) dakatar da dukkan tashi da saukar jiragen sama a yankin Fort Hancock da ke jihar Texas.
Asali: Legit.ng

