Yaki Ya Barke, Israila Ta kai Hari Kasar Iran, An Ji Fashe Fashe a Tehran
- Isra’ila ta kaddamar da abin da ta kira “harin riga-kafi” kan Iran a safiyar Asabar, a cewar Ministan Tsaro na kasar, Israel Katz, yayin da ta ayyana dokar ta-baci
- Gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci ne saboda tsammanin martanin Iran ta hanyar amfani da jiragen yaki marasa matuki da kuma makamai masu linzami
- An ji karar fashe-fashe da dama a birnin Tehran na kasar Iran, babban birnin kasar, yayin da aka kuma rawaito fashe-fashe a wasu wurare daban-daban
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Rahotanni sun nuna cewa kasar Yahudawa ta Isra'ila ta kaddamar da hare-hare kan Iran da safiyar Asabar, 28 ga Fabrairun 2026.
Hakan na zuwa ne bayan gaza cimma matsaya tsakanin Iran da Amurka a wata tattaunawa da suka yi a kasar Oman game da wasu abubuwa.

Source: Getty Images
Rahoton tashar Aljazeera ya nuna cewa a halin yanzu, babu wata sanarwa ta hukuma daga Iran game da harin da aka kai musu.
Hankula sun koma kan jin martanin da Iran za ta yi, da abin da Amurka za ta ce kasancewar ta sha alwashin kai hari kasar a baya.
Halin da ake ciki a kasar Iran
A bisa rahotannin da aka samu, an sanya asibitocin Iran cikin shirin ko-ta-kwana, an kuma tura motocin daukar marasa lafiya a wurare.
Mai magana da yawun ma’aikatar Lafiya ta Iran ya ce an sanya asibitoci cikin shirin ko-ta-kwana ne domin samun damar kula da wadanda za su iya samun rauni.
An samu karin bayani daga shugaban kwamitin tsaron kasa na Majalisar dokokin Iran, Ebrahim Azizi game da harin, inda ya ce:
“Mun gargade ku!”
“Yanzu kun shiga wata hanya da karshenta ba ya hannunku,”

Source: Getty Images
Iran na shirin mayar da martani
Wani jami'in Iran ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Tehran na shirin mayar da martani kan hare-haren Amurka da Isra’ila, inda ya ce martanin zai kasance mai tsanani matuka.
Rahotannin kafafen yada labarai na cikin gida sun ce an ji karar fashe-fashe a biranen Kermanshah, Lorestan, Tabriz, Isfahan da Karaj.
Iran ta rufe sararin samaniyarta
Mai magana da yawun hukumar sufurin jiragen sama ta Iran, Majid Akhavan, ya sanar a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Mehr cewa an rufe sararin samaniyar duk fadin kasar har sai an sake bayar da wata sanarwa.
A daya bangaren, ma’aikatar sufuri ta Iraki ta ce ta rufe sararin samaniyar kasar bayan hare-haren da aka kai wa Iran, a cewar wasu rahotanni.
Pakistan ta kai hari a Afghanistan
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin kasar Pakisatan ta sanar da cewa ta kai wasu jerin hare-hare babban birnin Afghanistan, Kabul.
Hakan na zuwa ne bayan sabani da kasashen ke samu a iyakokinsu, inda suka shafe kwanaki suna farmakar juna a 'yan kwanakin nan.
Gwamnatin Pakistan ta bayyana cewa za ta cigaba da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro a yankin, musamman a iyakokinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

