Australia: An Sanar da Ranar da Musulamai Za Su Fara Azumin Ramadan na 2026
- Babban mai bada fatawar kasar Australia ya sanar da ranar da za a fara azumin watan Ramadan na shekarar da muke ciki
- Ibrahim Mohamad ya bayyana cewa za a fara Sallar Tarawihi a daren Laraba da zarar jinjirin watan Ramadan ya ɓullo
- Yayi kira ga musulmai da su gudanar da ibada cikin kwanciyar hankali da yi wa kasashen duniya addu'ar zaman lafiya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Australia - Babban mai bada fatawa na ƙasar Australia, Ibrahim Mohamad, ya sanar da cewa watan azumin Ramadan na wannan shekarar zai fara ne a ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026.
Malam Mohamad, wanda shi ne shugaban Majalisar Fatawa ta Australia, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

Source: Getty Images
Sanarwar hakan ta biyo bayan tuntuɓar Limaman majalisar da aka yi sosai, inda aka yi nazarin lissafin bayyanar jinjirin watan na Ramadan, inji rahoton Khaleej Times.
Lissafin kimiyya kan bayyanar jinjirin wata
Babban mai bada fatawar, Ibrahim Mohamad ya ce:
"A Sydney, rana za ta faɗi ne da misalin ƙarfe 7:45 na yamma, yayin da za a haifi jinjirin wata da misalin karfe 11:01."
"A garin Perth kuwa, rana za ta faɗi ne da misalin ƙarfe 7:04 na yamma, inda za a haifi sabon watan da misalin ƙarfe 8:01."
Hakan na nufin cewa za a haifi sabon jinjirin watan ne bayan rana ta faɗi a Australia, don haka ba za a iya fara azumi a washe garin ranar ba.
Daren farko na sallah a sallar tarawihi
Ibrahim Mohamad ya kara da cewa:
"Daren farko na Ramadan da Sallar Tarawihi za su kasance ne a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, bayan faɗuwar rana."
Babban mai bada fatawar ya bayyana cewa hanyar da suke bi wajen ayyana farkon Ramadan tana dogara ne kan lokacin bayyanar jinjirin wata da ya danganci faɗuwar rana.
Babban mai bada fatawa Ibrahim Mohamad ya ce:
"Muna roƙon daukacin Musulmi da su girmama ra'ayoyin masana daban-daban kan wannan lamari domin tabbatar da haɗin kan al'umma baki ɗaya."
Kiran yin addu'o'in zaman lafiya
Mai fatawar ya yi kira ga Musulmi da su kula da azuminsu tare da yin addu'ar neman tsari ga ƙasashensu, zaman lafiyar duniya, da kuma sauƙaƙa raɗadi, in ji rahoton Premium Times.
"Musamman muna roƙon Allah ya kawo wa Musulmin Gaza-Palestine ɗauki, ya karɓi ibadunmu da azuminmu na wannan shekara baki ɗaya, ya albarkaci kowa," in ji Ibrahim Mohamad

Source: Getty Images
Muhimmanci azumin watan Ramadan
Ramadan shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, wanda Musulmi a duk faɗin duniya ke azumta tare, cikin addu'o'i, bauta, da kuma taimakon mabuƙata.
Azumi yana ɗaya daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar, tare da kalmar shahada, salloli biyar, bayar da zakka, da kuma gudanar da aikin Hajji idan da hali.
A shekarar da ta gabata, tsawon lokacin azumi a sassan duniya ya kasance tsakanin sa'o'i 10 zuwa 20 a kowace rana, ya danganta da yankin da mutum yake.

Kara karanta wannan
An gano matsalar da za a iya samu a zaben shugaban kasar 2027 saboda azumin Ramadan
Ranar fara duba watan Ramadan a Saudiyya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Saudiyya ta bukaci musulmi da su fara duba jinjirin watan Ramadan a yammacin Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026.
Idan har an ga watan a ranar Talata, to za a fara azumin Ramadan ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, kamar yadda sanarwa ta nuna.
Idan ba a ga watan ba, to watan Sha'aban zai cika kwanaki 30, sannan a fara azumin Ramadan a ranar Alhamis, 19 ga watan na Fabrairu.
Asali: Legit.ng

