Sojan Amurka Dan Asalin Najeriya Ya Nutse a Teku bayan Fadowa a Jirgin Yaki

Sojan Amurka Dan Asalin Najeriya Ya Nutse a Teku bayan Fadowa a Jirgin Yaki

  • Rahotanni sun nuna cewa sojan kasar Amurka ɗan asalin Najeriya, Chukwuemeka Oforah ya rasu bayan fadowa daga jirgi zuwa cikin teku
  • Rundunar sojan ruwan kasar ta tabbatar da rasuwar shi a ckin tekun Caribbean bayan shafe sa'o'i ana nemansa ba tare da cimma nasara ba
  • An bayyana cewa matashin ya rasu yana da shekara 21 da haihuwa kuma ya kasance yana zaune a jihar Florida ta kasar Amurka kafin ya rasu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - An tabbatar da mutuwar sojan Amurka ɗan asalin Najeriya, Chukwuemeka Oforah, bayan mummunan lamari da ya faru, inda ya faɗa cikin teku daga jirgin ruwan yaƙi mai suna USS Iwo Jima a Caribbean.

An ruwaito cewa ya faɗa teku daga jirgin ne da yammacin ranar 7 ga Fabrairu, 2026, yayin gudanar da ayyukan yau da kullum, inda aka neme shi aka rasa.

Kara karanta wannan

Bayan turo sojoji, Amurka za ta kafa 'tashar jiragen yaki' a a jihar Arewacin Najeriya

Jirgin sojan ruwan Amurka
Wani jirgin sojan Amurka a cikin teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Dan Najeriya ya mutu a Amurka

Rahoton BBC ya nuna cewa an tabbatar da mutuwar sojan ne bayan an kammala bincike da nemansa da aka dakatar a ranar 10 ga Fabrairun 2026.

An sanar da mutuwarsa a ranar Laraba, kuma har yanzu sojoji na ci gaba da bincike kan lamarin, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Rahoton ya ce mutuwar Oforah ita ce ta farko da aka samu cikin sojojin Amurka a ƙarƙashin shirin Operation Southern Spear na gwamnatin Shugaba Donald Trump, wanda ke kai hari kan kwale-kwalen safarar miyagun ƙwayoyi.

Oforah, wanda aka tura zuwa Bataliya ta 3, Runduna ta 6 ta Marine daga Camp Lejeune a Carolina, yana cikin tawagar wasu sojoji na musamman da ke jirgin Iwo.

An ce ya shiga rundunar sojin Amurka ne a watan Oktoba 2023, sannan ya kammala horonsa a makarantar sojojin kasar a watan Fabrairu 2024.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump a White House. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maganar sojojin ruwan Amurka

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro ta jero abubuwan da sojojin Amurka 200 za su yi idan suka shigo Najeriya

Sanarwar da Rundunar Sojojin Ruwan Amurka ta fitar ba ta bayyana yadda ya faɗo daga jirgin ba, amma ta miƙa ta’aziyya ga iyalansa.

Fox New ta rahoto cewa rundunar ta ce:

“Dukkanmu muna cikin alhini, muna tare da iyalan Oforah.
“Rashin Lance Cpl. Oforah abin takaici ne ga dukkan rundunar sojin ruwa. Za a yi kewarsa ƙwarai, kuma ba za a manta da jajircewarsa wajen aiki ba,”

In ji Kanar Tom Trimble, kwamandan rundunar sojin Amurka da aka fi sani da SOC.

Wata sanarwa daga rundunar ta ce an yi aikin neman sojan da kayan aiki da suka haɗa da jiragen ruwa guda biyar da jiragen sama 10 domin ceto shi.

An kashe 'yan Najeriya a Ukraine

A wani rahoton, kun ji cewa Rundunar sojin kasar Ukraine ta wallafa wata sanarwa da ke nuna cewa ta kashe wasu 'yan Najeriya biyu.

Dakarun Ukraine sun ce sun kashe mutanen ne bayan shiga cikin rundunar sojojin Rasha a yakin da ake gwabzawa tsakanin kasashen.

A wani bayani da ta yi, Ukraine ta yi zargin cewa kasar Rasha ba ta ba sojojin da ta dauko daga Najeriya cikakken horon da za su fafata a fagen daga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng