2026: Saudiyya Ta Sanar da Ranar da Musulmi Za Su Fara Duba Watan Azumin Ramadan
- Kasar Saudiyya ta bukaci musulmi da su fara duba jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026
- Idan har an ga watan a ranar Talata, to za a fara azumin Ramadan ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, kamar yadda sanarwa ta nuna
- Idan ba a ga watan ba, to watan Sha'aban zai cika kwanaki 30, sannan a fara azumin Ramadan a ranar Alhamis, 19 ga watan na Fabrairu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Saudiyya - Yayin da watan Ramadan na 2026 ya gabato, Saudiyya ta bukaci al'ummar Musulmi a kasar da su fara duban watan azumin na bana.
An bukaci Musulmi su fara duba watan Ramadan din ne daga ranar 29 ga Sha'aban, 1447 AH, wanda zai yi daidai da 17 ga Fabrairu, 2026.

Source: Getty Images
An sanya ranar fara duba watan Ramadan
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da shafin watsa labaran masallaci mai tsarki na Inside the Haramain ya wallafa a shafinsa na X a ranar 10 ga Fabrairu, 2026.
Sanarwar ta ce:
"Za a fara duba watan Ramadan 1447 daga yammacin ranar Talata, 29 ga watan Sha'aban 1447, wanda ya yi dai dai da 17 ga Fabrairu, 2026."
Idan har aka ga watan a wannan rana, kuma kwamitin koli na ganin watan ya tabbatar da hakan, to Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026 za ta zama 1 ga watan Ramadan, 1447AH.
Amma idan ba a samu damar ganin watan ba, hakan na nufin watan Sha'aban zai cika kwanaki 30, sannan Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026 ta zama 1 ga watan Ramadan, 1447AH.
Karanta sanarwar a nan kasa:
Ramadan: Saudiyya ta yi kira ga Musulmi
A wata sanarwa da kwamitin Kotun koli na ganin wata ya fitar, wadda jaridar Times of India ta gani, Saudiyya ta sanar da cewa:
"Kotun ta bukaci duk wanda ya ga watan da idonsa ko da madubin hangen nesa, ya garzaya ofishin kwamitin mafi kusa domin bayar da shaidarsa."
Sanarwar ta kara da cewa ana fatan wadanda Allah ya ba su ikon duba watan za su hada kai da kwamitin da aka kafa.
Wannan aiki ne na neman lada daga Allah Madaukakin Sarki saboda taimakon Musulmi baki daya wajen gudanar da ibadar azumi a fadin duniya.

Source: Getty Images
Muhimmancin duba wata a Saudiyya
Ba a yanzu ne aka fara al'adar duba wata a Saudiyya ba. Duk shekara, kwamitin koli na duban watan na aika sako ga daukacin Musulmin kasar game da bukatar duba jinjirin wata a kwanakin karshe na Sha'aban.
Wannan al'ada ce da kasar take gudanarwa a kowace shekara, ba wai kawai don watan Ramadan ba, har ma da sauran watanni, musamman watan Shawwal da ake duba ranar sallah.
Ganin watan shine babban ma'aunin da yake nuna farkon azumi a yawancin kasashen duniya, musamman wadanda suke bin sahun kasar Saudiyya.
Idanuwan daukacin Musulmin duniya yanzu haka suna kan kasar ta Saudiyya domin jin sanarwar da za ta fito daga fadar masarautar nan ba dadewa ba.

Kara karanta wannan
'Kiran Allah': Saudiyya ta fadi ranar da za ta fara ba da bizar aikin Hajjin 2026
Hasashen ranar fara Azumi na 2026
Tun da fari, mun ruwaito cewa, ana sa ran al'ummar Musulmi za su fara azumin Ramadan na shekarar 2026 ne a ranar 19 ga watan Fabrairu cikin yanayin sanyi.
Sa'o'in da Musulmi za su dauki azumi zuwa shan ruwa za su kasance matsakaita tsakanin awa 12 zuwa 13 a mafi yawan kasashen duniya a shekarar bana.
Yanayin kaka da sanyi zai taimaka wa Musulmi gudanar da ibada cikin sauki ba tare da fuskantar tsananin kishirwa ko wahalar zafi ba, sabanin yadda aka yi a bara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

